An sako Sarkin Bukkuyum da aka sace a Zamfara
Mai martaba Sarkin Bukkuyum da ke Jihar Zamfara Alhaji Muhammad Usman da wasu ’yan bindiga suka sace da dare a ranar Juma’ar da ta gabata ya samu kansa, inda ya koma gida bayan kwana hudu da sace shi. Bayanan da gidan rediyon Faransa ya samu sun ce an biya diyyar Naira miliyan 10 kafin a […]
Mai martaba Sarkin Bukkuyum da ke Jihar Zamfara Alhaji Muhammad Usman da wasu ’yan bindiga suka sace da dare a ranar Juma’ar da ta gabata ya samu kansa, inda ya koma gida bayan kwana hudu da sace shi.
Bayanan da gidan rediyon Faransa ya samu sun ce an biya diyyar Naira miliyan 10 kafin a sako Sarkin wanda aka ce an boye shi a garin Gadar Zaima da ke Jihar Zamfara.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar ASP Sanusi Amiru ya tabbatar da sako Sarkin amma kuma ya ki ya bayyana cewa an biya diyya kafin sakin nasa.
An sace Sarkin ne a ranar Juma’ar da ta gabata da misalin karfe 7:55 na dare lokacin da yake zaune a masallaci yana jirar a gudanar da Sallar Isha’i.
Sakataren Masarautar Bukuyum Alhaji Aliyu Muhammad ya bayyana wa wakilinmu kwana daya bayan sace Sarkin cewa, Sarkin ya bukaci a yi masa addu’a bayan da wadanda suka sace shi haka, suka yi amfani da daya daga cikin wayoyin da suka kwace a Masallacin kofar Fadar Sarkin da ke Bukkuyum suka sanya ya yi magana da iyalinsa. “Daga baya sun ce yana son ya yi magana da ni, mun yi magana kuma cikin abin da yake cewa shin ne kada a neme shi yana cikin koshin lafiya, amma bai san inda yake ba a halin yanzu, a dai ci gaba da yi masa addu’a, kamar yadda ya yi umarni,” inji shi.
Mutanen da suka sace Sarkin an ce sun je ne a cikin wata mota kirar Honda suka tsaya a kofar masallacin mutum biyar suka fito, suka nemi tafiya da shi.
Majiyarmu ta ce da fitowarsu sai suka shiga masallacin suka haska fuskar Sarkin da tocila, sai daya daga cikinsu ya ce masa tashi mu tafi cikin mota, sai Sarkin ya tambaye su ina za mu je, suka ce tashi dai mu tafi, haka dai aka rika ja-in-ja a tsakaninsu.
kanen Sarkin shakiki, Alhaji Muhammad Kabir da abin ya faru a gabansa ya ce bayan sun ce Sarki ya bi su, sai na ce “Haba babu ko gaisuwa ku ce Sarki ya tashi ya bi ku? Jin haka sai suka fara harbi a sama suka ce duk mu kwanta mu kawo wayoyinmu. Sai muka ce ba mu da wayoyi mun kai su caji har da wayar Sarki, suka ce idan muka same ku da waya za mu harbe ku, wannan ya ba su damar tafiya da sarki cikin mota.”
Alhaji Kabir ya ce bayan sun sanya Sarkin a cikin mota sai wasu suka leka masallaci suka ga yara suna karatu amma ga wayoyi suna caji, sai suka ce malaminsu ya ba su wayoyin, sai ya ce, wayoyin dalibai ne, sai wani daga cikinsu ya dauki uku daga ciki, nan suka rika harbi har suka tafi da shi.
Sakataren Masarautar ya ce yana gida lamarin ya faru, amma da aka sanar da shi sun dauki mota sun bi hanya suka wuce har garin Anka wurin Mai martaba Sarkin Zamfaran Anka Alhaji Attahiru Ahmad don sanar da shi halin da ake ciki, “Daga bisani sai muka shiga daji tare da motoci da babura, amma har wayewar garin Asabar babu wani labara, a daji muka kwana wajen nemansa.
Sarkin Anka Alhaji Attahiru Ahmad da yake zantawa da wakilinmu a fadarsa, ya ce wannan ba karamin al’amari ba ne, kuma ba za a ce bai taba faruwa ba, sai dai bai taba faruwa a Jihar Zamfara ba, inda ya bukaci a yi ta addu’o’in Allah Ya bayyanar da Sarkin.
Sarkin ya ce har zuwa lokacin wadanda suka sace Sarkin ba su bukaci kudi ba, sai dai ba a san abin da gaba za ta yi ba.