An sako wadda aka yi kuskuren ɗaure ta bayan shekara 43 a kurkuku

Shari’ar Sandra ita ce mafi daɗewa da aka yi kan kuskure ga wata mata a tarihin Amurka.

An sako wadda aka yi kuskuren ɗaure ta bayan shekara 43 a kurkuku

Wata tsohuwa mai shekara 63, mai suna Sandra ‘Sandy’ Hemme, ’yar ƙasar Amurka da aka ɗaure a kurkuku kan kisan kai, an soke hukuncin bayan ta shafe shekara 43 saboda kisan da ba ta aikata ba.

A cewar jaridar The Guardian, an yanke wa Hemme hukunci ne a 1985 bisa la’akari da kalamanta na cin zarafi da ta yi yayin da take jinyar ciwon taɓin hankali.

Sai dai yanzu alƙali ya yanke hukuncin cewa akwai shaidu da gamsassun hujjojin da ke nuna cewa wacce aka yanke wa hukuncin ba ta da wani laifi.

An dai yanke wa Sandra Hemme hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan kisan wata ma’aikaciyar ɗakin karatu a 1980, mai suna Patricia Jeschke, a St Joseph, da ke Jihar Missouri.

Alƙalin kotun Gundumar Liɓingston Mai shari’a Ryan Horsman ya yanke hukuncin cewa “shaida kai-tsaye” ta alaƙanta kisan Patricia da wani ɗan sandan yankin wanda daga baya ya tafi kurkuku saboda wani laifi kuma ya riga ya mutu.

Alƙalin ya ce Sandra wadda ta shafe shekara 43 a gidan yari, dole a sake ta cikin kwana 30 sai dai idan masu gabatar da ƙara sun yanke shawarar sake yi mata gwaji.

Hukuncin da alƙalin ya yanke ya biyo bayan da lauyoyin Sandra suka gabatar da shaidun da ke alaƙanta kisan da tsohon ɗan sandan yankin mai suna Michael Holman.

Shari’ar Sandra ita ce mafi daɗewa da aka yi kan kuskure ga wata mata a tarihin Amurka.

Lauyoyinta, sun ce hukumomi sun yi watsi da kalaman da Sandra ta yi masu cin karo da juna kuma sun kasa bayyana shaidar da za ta taimaka wajen kare ta.

Da farko Sandra ta amsa laifin kisan kai don guje wa hukuncin kisa, amma daga baya aka soke hukuncin da aka yanke mata a kan ɗaukaka ƙara. Ta sake ɗaukaka ƙara a 1985.

A cikin hukuncin mai shafuka 147, lauyoyinta da ke neman a wanke ta sun yi zargin cewa hukumomi sun yi watsi da wannan saɓani.

A lokacin da Sandra take da shekara 20 tana fuskantar jinya kan matsalar rashin gani kuma tana amfani da ƙwayoyi.

Lauyoyinta sun lura cewa tana da tarihin jinyar taɓin hankali, inda ta shafe mafi yawan rayuwarta tana jinya tun tana da shekara 12.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos