An sako wani malami dan Afirka ta Kudu da aka tsare a Masar
An sako wani malamin addinin Musulunci mazaunin Afirka ta Kudu da aka tsare a Masar sama da shekara daya ba tare da gabatar da shi a gaban kotu ba.Iyalai da abokan malamin mai suna Sheikh AbdusSalaam Bassiouni ma shekara 65 da yake da takardun zama dan Afirka ta Kudu da Masar kuma yake zaune a […]
An sako wani malamin addinin Musulunci mazaunin Afirka ta Kudu da aka tsare a Masar sama da shekara daya ba tare da gabatar da shi a gaban kotu ba.
Iyalai da abokan malamin mai suna Sheikh AbdusSalaam Bassiouni ma shekara 65 da yake da takardun zama dan Afirka ta Kudu da Masar kuma yake zaune a Afirka ta Kudu tun 1990 ne suka bayyana sako shi.
Kafar sadarwa ta Times Libe ta Afirka ta Kudu ta ce an tsare Bassiouni da dansa Bilal ne a filin jirgin sama na Alkahira a shekarar 2014 inda aka tuhume su da kasancewa ’ya’yan kungiyar Ihkwanul Muslimina wata kungiyar siyasa ta mabiya Sunnah da aka haramta a Masar. An saki Bilal bayan awa 20 da tsare shi, amma aka ci gaba da tsare mahaifinsa a kaso ba tare da gabatar da shi a gaban kotu ba, kamar yadda iyalansa suka bayyana.
Sheikh Bassiouni ya je Masar ne don halartar aure ’yarsa lokacin da aka kama shi.
Kakakin Sashin Hulda da kasashen Waje na Afirka ta Kudu Nelson Kgwete, ya fadi ta shafin tweeter cewa ba a sanar da gwamnatin kasar a hukumance kan sako Bassiouni ba, kuma mahukuntan Masar sun nace cewa malamin dan kasar Masar ne.
A baya sashin ya ce ya gaza taimaka wa iyalan Bassiouni ne kan lamarin saboda Masar ta kama shehin malamin ne a matsayin dan kasarta kuma ta hana hukumomin Afirka ta Kudu isa gare shi.
A shekarar 2013 ne aka haramta kungiyar Ikhwanul Muslimina bayan kifar da gwamnatin tsohon Shugaban Masar Mohammed Morsi wanda dan kungiyar ne.
A ranar Talatar da ta gabata ce kungiyar neman a sako Bassiouni ta bayyana sako malamin, a shafinta na Facebook.
Bilal ya ce ya yi magana da mahaifinsa ta kafar sadarwar Skype kuma ya fahimci ya galabaita. “Hakika akwai matsala game da lafiyarsa,” inji Bilal.
Kuma a cewar kafar ta Times Libe, an watsa hotunan sako malamin a kafofin sadarwar Intanet.