An sako ‘yar uwa da mai taimakawa shugaban Bwari da aka sace a Abuja
Masu garkuwa da mutane sun sako wasu mata biyu da suka sace a yankin Karamar hukumar Bwari a Abuja a ranar bikin sabuwar shekara. Matan biyu jami’ai ne masu maitaimakawa shugaban Karamar hukumar Dokta John Gabaya, a kan siyasa da kuma wata ‘ya ga Dan uwansa, an sako su ne a ranar Asabar bayan biyan […]
Masu garkuwa da mutane sun sako wasu mata biyu da suka sace a yankin Karamar hukumar Bwari a Abuja a ranar bikin sabuwar shekara.
Matan biyu jami’ai ne masu maitaimakawa shugaban Karamar hukumar Dokta John Gabaya, a kan siyasa da kuma wata ‘ya ga Dan uwansa, an sako su ne a ranar Asabar bayan biyan kudin fansa, kamar yadda Aminiya ta samu labari.
An sace matan biyu ne a lokacin da suka je kauyen Tokolo mahaifar jagoran da ke kusa da Garin Bwari inda yake karban gaisuwar murnar sabuwar shekara, a ranar.
Haka Aminiya ta samu labarin cewa wani Dan uwan jagoran mai suna Ibro Shakogaza da ake kyautata zaton shi ne a ke nema, ya samu nasarar tserewa.
Babban jami’in ‘yan sanda na garin, CSP Biyodun Makanjuola wanda ya tabbatar da faruwan lamarin, ya ce sun fara gudanar da bincike a kai.