An salami dan Obasanjo daga asibiti

An salami dan tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo da mayakan Boko Haram suka harba daga asibiti a shekaranjiya Laraba.Laftana Kanar Adeboye Obasanjo ya samu rauni a garin Bazza da ke Arewacin Jihar Adamawa a lokacin da sojojin Najeriya suka yi yunkurin sake kwato garin da ’yan Boko Haram suka kwace.An kai shi Cibiyar Lafiya ta […]

An salami dan Obasanjo daga asibiti
An salami dan Obasanjo daga asibiti

An salami dan tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo da mayakan Boko Haram suka harba daga asibiti a shekaranjiya Laraba.
Laftana Kanar Adeboye Obasanjo ya samu rauni a garin Bazza da ke Arewacin Jihar Adamawa a lokacin da sojojin Najeriya suka yi yunkurin sake kwato garin da ’yan Boko Haram suka kwace.
An kai shi Cibiyar Lafiya ta Tarayya inda ya yi kwana biyu yana jinya. Wani babban jami’in asibitin ya shaida wa Aminiya cewa, “Ya samu karamin rauni kuma an yi masa jinya an sallame shi. Ya samu kula sosai da za mu iya bayarwa, kuma ya samu sauki cikin gaggawa.”
Har wa yau matsalar tsaro na cikin dalilan hanzarta sallamarsa inji majiyar inda ta ce manyan jami’an soja ne suka ba da shawarar a sallame shi domin a fitar da shi daga jihar.
Kakakin asibitin Malam Adamu Dodo ya tabbatar da labarin, inda ya ce, saurin samun sauki da batun tsaro sun taka wara wajen hanzarta sallamarsa.
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da Mukaddashin Gwamnan Jihar Ahmadu Umar Fintiri na daga cikin wadanda suka je duba shi a asibiti.
Aminiya ta samu labarin cewa mayakan Boko Haram sun ci karfin Laftana Kanar Obasanjo da sauran hafsoshin soja ne bayan da sojojin da ke karkashinsu suka ki bin umarnin kwamandojinsu.
Majiyarmu ta ce, lokacin da sojojin suka hadu da mahara a Bazza, kwamandojinsu sun ba su umarnin su yake su amma suka gaza yin hakan yadda ya kamata. Mayakan na bude musu wuta sai suka ranta a na kare ba tare da tsayawa su mayar da martini kamar yadda manyansu suka umarce su ba.
Ya ce, wannan ne ya sa aka kashe wasu sojoji, aka raunata wasu ciki har da dan Obasanjo, kuma ya ce har yanzu Bazza da Michika da Gulak da Madagali suna karkashin ikon ’yan Boko Haram.