An sallami Anthony Joshua daga asibiti
Hatsarin ya yi sanadin rasuwar mutane biyu daga cikin tawagar fitaccen ɗan wasan damben.
An sallami fitaccen ɗan wasan damben duniya, ɗan asalin Najeriya daga asibitin Duchess International Hospital da ke Ikeja, a Jihar Legas, bayan hatsarin mota da ya yi.
Hatsarin mota ya rutsa da Joshua a kan hanyar Legas zuwa Ibadan wanda ya yi sanadin rasuwar abokan aikinsa, Lateef Ayodele da Gami Cina.
- Yadda sabbin dokokin haraji za su shafi ’yan Najeriya a 2026
- Fitattun Jaruman Kannywood da suka riga mu gidan-gaskiya a 2025
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Legas, Gbenga Omotoso, da Hadimin Gwamnan Ogun, Kayode Akinmade, sun tabbatar da cewa Joshua yana murmurewa a gida.
A cikin sanarwar, an ce Joshua da mahaifiyarsa sun je Legas don yin bankwana da waɗanda suka rasu kafin kai gawarwakin ga iyalansu.
Gwamnan Jihar, Babajide Sanwo-Olu, da na Ogun, Dapo Abiodun, sun gode wa jama’a bisa nuna damuwa da goyon baya.
Sun kuma gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma ƙungiyar likitoci a Lagoon Hospital, Ikoyi, bisa kulawa da ƙwarewar da suka nuna.