An sallami fursunoni don rage cunkoso a gidajen yari a Yobe
Ya shawarci alƙalai da kotuna da su kasance masu bin doka a koyaushe yayin gudanar da ayyukansu.
Babban alkalin Jihar Yobe, Mai Shari’a Kaigama Umar, ya sallami wasu fursunoni bakwai tare da bayar da belin wasu fursunonin guda 14 a cibiyoyin gyaran hali a garuruwan Potiskum da Gashuwa da Nguru.
Mai Shari’a Kaigama wanda kuma shi ne shugaban kwamitin da ke sa ido kan shari’ar miyagun laifuka ya yantar da fursunonin ne a ziyarar da ya kai gidajen gyaran halin da ke jihar.
- Matashin da ya sare hannun kanen mahiafinsa ya shiga hannu
- Mutanen gari sun kama mai garkuwa da mutane a Jos
Babban alƙalin jihar ya samu rakiyar mambobin kwamitin zuwa wasu cibiyoyin gyaran halin.
Ya ci gaba da cewa ziyarar nada nufin rage cunkoso a gidajen gyaran hali da kuma duba halin da fursunonin ke ciki a jihar.
Waɗanda aka sallama ɗin dai fursunoni shida ne daga matsakaicin gidan gyaran hali da ke Potiskum da kuma ɗaya daga Gashuwa da ya shafe sama da wata shida ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ba.
Yayin da uku daga fursunonin aka sallama daga gidan gyaran hali na garin Nguru, huɗu kuma aka ba da belin su daga gidan gyaran hali na Potiskum.
Mai shari’a Kaigama ya bayar da tabbacin ci gaba da haɗa kai da Ofishin Kwamishinan Shari’a wajen taimaka wa gidan gyaran hali a jihar da kuma jin daɗin fursunonin jihar Yobe baki ɗaya.
Ya kuma shawarci alƙalai da kotunan shari’a da su kasance masu bin doka a koyaushe yayin gudanar da ayyukansu ba tare da tsoro ko fargaba ba.
Haka nan ya kuma buƙace su da su rage hukuncin da ba dole ba kuma su jaddada kan hukuncin da ba na tsarewa ba, yin tara da kuma yin hukunci a matsayin mafita ta ƙarshe.
Aminiya ta ruwaito cewa wannan na zuwa ne a ƙoƙarin da Gwamnatin Yobe ke yi na rage cinkoso a gidajen gyaran hali da ke jihar.