An sallami Kwamishinar Mata ta Jihar Bauchi daga aiki

Sallamar Hajiya Zainab Baban Takko daga matsayin Kwamishina ya fara aiki ne nan take, a cewar gwamnatin jihar Bauchi

An sallami Kwamishinar Mata ta Jihar Bauchi daga aiki

Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi, ya sallami Kwamishinar Harkokin Mata da Ci-gaban Yara, Zainab Baban Tanko.

Sanarwar da kakakin gwamnan, Mukhtar Giɗaɗo, ya fitar ta bayyana cewa sallamar ta fara aiki ne nan take.

Ya bayyana cewa hakan ta faru ne a sakamakon sauye-sauye a majalisar zartarwa ta Jihar Bauchi.

Ya bayyana godiyar Gwamna Bala ga tsohuwar Kwamishinar bisa gudummawar da ta bayar ga ci-gaban jihar, tare da yi ,ta fatan alheri.