An sallami likitan Michael Jackson daga gidan yari
Likitan marigayi Michael Jackson, Conrad Murray, wanda kuma aka tuhume shi da laifin sanadiyyar mutuwar mawakin, ya samu kansa a Litinin da ta gabata, bayan da kotu ta wanke shi daga laifi kuma aka sallame shi.Likitan, wanda a can baya aka yanke wa hukuncin daurin shekara hudu a gidan yari kuma ya kwashe shekara biyu […]

Likitan marigayi Michael Jackson, Conrad Murray, wanda kuma aka tuhume shi da laifin sanadiyyar mutuwar mawakin, ya samu kansa a Litinin da ta gabata, bayan da kotu ta wanke shi daga laifi kuma aka sallame shi.
Likitan, wanda a can baya aka yanke wa hukuncin daurin shekara hudu a gidan yari kuma ya kwashe shekara biyu a daure, an sallame shi ne da misalin karfe 12:01 na dare, kamar yadda hukumar tsaro ta Amurka ta tabbatar, a sakamakon sauyi da aka samu a kundin tsarin dokokin laifuffuka na birnin Los Angeles.
A 2011 ne aka yanke wa likitan hukunci, bayan da kotu ta same shi da laifin haddasa mutuwar mawaki Michael Jackson, wanda ya mutu a watan Yuni, 2009. An samu shaidar da ta tabbatar da dewa likitan ne ya ba shi maganin sanya barci mai karfin gaske, wanda shi ne ya haddasa rikicewar jikinsa kuma ya haddasa mutuwar tasa.