An sallami hadimar Aisha Buhari daga aiki
Sani Zorro tsohon fitaccen dan jarida ne kuma tsohon shugaban kungiyar ’yan jarida ta Najeriya da ma ta Afirka ta Yamma.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sallami Zainab Kazeem daga mukaminta na Hadimar Matar Shugaban Kasa kan Turaka.
Buhari ya kuma nada tsohon fitaccen dan jarida kuma tsohon Majalisar Wakilai, Muhammad Sani Zorro, a matsayin Babban Hadimin Matar Shugaban Kasa kan Hulda da Jama’a da Tsare-tsare.
- Zaben 2023: Kalubalen da ke gaban Saraki
- Za a fara biyan mata masu juna biyu N5,000 duk wata a Jigawa
Sanarwar da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar ta ce sallamar Zaina Kazeem tar fara aiki ne daga ranar Juma’a 11 ga watan Fabrairu, 2022.
Garba Shehu ya ce Buhari ya kuma sauya wa wasu hadiman Asiha Buhari wurin aiki zuwa Ofisihin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha.
Sanarwar ta ce hadiman matar shugaban kasa da za ta bukaci a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya tura su zuwa wasu hukumomi a ma’aikatu su ne Dokta Mohammed Kamal Abdulrahman and Hadi Uba, da kuma Wole Aboderin.
Sani Zorro tsohon fitaccen dan jarida ne kuma tsohon shugaban kungiyar ’yan jarida ta Najeriya da ma ta Afirka ta Yamma.