An sallami Sarkin Daura daga asibiti   

Ranar Alhamis da rana ne aka sallami Mai martaba Sarkin Daura Dokta Farouk Umar Farouk daga asibitin kwararru na gwamnatin tarayya bayan kwashe kwanaki bakwai yana jinya. Sarkin dai ya yi fama da jinyar hawan jini a asibitin kafin daga bisani a sallame shi. A farkon jinyar ta shi ce aka rika yada jita-jitar cewa […]

An sallami Sarkin Daura daga asibiti   

Sarkin Daura, Dokta Farouk Umar Farouk

Ranar Alhamis da rana ne aka sallami Mai martaba Sarkin Daura Dokta Farouk Umar Farouk daga asibitin kwararru na gwamnatin tarayya bayan kwashe kwanaki bakwai yana jinya.

Sarkin dai ya yi fama da jinyar hawan jini a asibitin kafin daga bisani a sallame shi.

A farkon jinyar ta shi ce aka rika yada jita-jitar cewa ya kamu da cutar COVID-19, wacce ta yi sanadiyyar kai shi asibitin.

Sai dai masarautar ta musanta rahoton da aka yi ta yada yadawa lokacin, kuma babu wani bayani akan haka a hukumance.

Sarkin ya fita daga harabar asibitin inda yake dagawa sauran marasa lafiya da masu jinyarsu hannu a cikin yanayi na tausayawa.