An sallami sojar da ta zargi shugabanta da neman lalata da ita

Rundunar Sojin Ƙasan Najeriya ta sallami wata ƙurtu sojan da ta zargi wani babban soja da yunƙurin yin lalata da ita

An sallami sojar da ta zargi shugabanta da neman lalata da ita

Rundunar Sojin Ƙasan Najeriya ta sallami wata ƙurtu sojan da ta zargi wani babban soja da yunƙurin yin lalata da ita.

Rundunar ta ce ta sallami ƙaramar dokar mai muƙamin Private daga aiki ne bayan ta kammala bincike kan zargin da ta yi.

Kakakin rundunar, Onyema Nwachukwu, ya bayyana cewa bayan kammala zuzzurfan binciken da aka gudanar, an gano cewa babu ƙamshin gaskiya a zargin da Private Ruth Ogunyele ta yi wa Kanar I.B Abdulkareem.

Onyema Nwachukwu ya cewa,  hasali ma binciken ya gano cewa Private Ruth Ogunyele ta samu taɓin ƙwaƙwalwa.

A sakamakon haka ne rundunar ta yanke shawarar sawwaka mata daga aikin soji.

Amma ya ce duk da sallamar ta daga aiki da aka yi, za a biya ta kudaden garatuti kuma za ta rika karɓar fansho.

A watan Janairu ne Ruth Ogunyele ta zargi Kamar I.B Abdulkareem da yunƙurin yin lalata da ita.

A wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Tiktok, Ruth Ogunyele ta bayyana ta zargi Abdulkareem da Kanar G.S Ogor, da kuma Birgediya-Janar I.B Solebo, da ƙuntata mata.

A cewarta, Kamar Abdulkareem ya sha yunƙurin yin lalata da ita, ta hanyar yi mata allura ba da son ranta ba da kuma fitar da ita daga gidan da take zaune da kuma killace ta a asibitin masu taɓin hankali, na tsawon watanni saboda ta ki amincewa ya yi lalata da mata.

A sakamakon zargin ne a lokacin Ma’aikatar Harkokin Mata ta buƙaci Babban Hafsan Rundunar Sojin Ƙasan Najeriya, Laftanar-Janar Tarooed Lagbaja ya gudanar da cikakken bincike a kan lamarin.

Amma a jawabinsa kan sakamakon binciken, kakakin rundunar, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, ya ce an gano cewa wanda Ogunleye take zargi bai aikata laifin ba.

Nwachukwu, ya ce, ”Rundunar ta gudanar da zuzzurfan bincike kan duk zarge-zargen da kuma hujjoji da shaidun da aka gabatar domin gano gaskiya da tabbatar da adalci.

“Binciken ya gano cewa Kanar IB Abdulkareem bai ci zarafin Private Ruth Ogunyele ta hanyar lalata ba, kamar yadda ta yi zargi.”

A cewarsa, tun bayan gano cewa Ruth Ogunyele tana da matsalar ƙwaƙwalwa a shekarar 2022 rundunar yanke shawarar sallamarta daga aiki.

Amma duk da haka rundunar ta ɗauki ɗawainiyar cewa ta samu cikakkiyar kulawar lafiya ta samu sauƙi ta sallame ta koma cikin al’umma.

A cewarsa, “a lokacin da akentsal da bincike kan zargin da ta yi ne aka gano wasu abubuwa, lura da yadda dabi’unta na yau da kullum da ma a kafofin sada zumunta suma sauya.

“Haka ya haifar da shakku game da cikar lafiyarta da cikar hankalinta.”

Ya ce bayan an yi mata gwaji a asibitin sojoji an gano cewa ta samu matsalar ƙwaƙwalwa.

“Asakamakon haka ne aka yi mata gwaje-gwaje a Asibitin Kasa da ke Abuja, inda sakamakon gwajin ya nuna cewa tana da matsalar.

Manjo-Janar Nwachukwu ya ce, ganin cewa ga halin Ruth da take ciki, rundunar ta yanke shawarar yin rangwame da kuma jingine hukuncin da ya kamata a yi wa mata.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7