An sallamo Trump daga asibiti bayan yunƙurin halaka shi

Shugabannin duniya sun shiga aikewa da Donald Trump sakon jaje

An sallamo Trump daga asibiti bayan yunƙurin halaka shi

An sallamo tsohon Shugaban Amurka Donald Trump daga asibiti bayan harbinsa da bindiga da aka yi a wani taron yaƙin neman zaɓe.

Bayanai sun ce wani ɗan bindiga ne ya buɗe wuta a wurin yaƙin neman zaɓen a Jihar Pennsylvania, lokacin da yake yi wa dubban magoya bayansa jawabi.

Hukumar Tsaron ta FBI ta bayyana sunan maharin da Thomas Matthew Crooks mai shekara 20 da tuni an harbe shi a yayin da yake buɗe wutar.

Nan da nan dai jami’an leken asirin suka yi wa tsohon shugaban ƙasar rumfa tare da lullube shi a yayin da suka kai masa ɗauki.

Hotunan bidiyo da suka karade dandalin sada zumunta na X sun nuna yadda tsohon shugaban ƙasar ya yi gaggawar sunkuyawa tare da riƙe ɓarin kunnensa na dama inda aka harba yana kwararar da jini.

Sai dai gabanin jami’an tsaro su ɗauke shi daga kan dandamalin da yake jawabi, ya ɗaga hannu da alamar jinjina domin magoya bayansa su tabbatar bai karaya ba.

Wannan lamari dai ya faru ne a yayin da zaɓen shugaban Amurka ke ƙaratowa kuma wasu manyan jiga-jigai a jam’iyyar Democrat na ƙara nuna adawa ga takarar Shugaba Joe Biden yayin da shi kuma ke cewa babu gudu babu ja da baya.

Shugabannin duniya sun yi wa Trump jaje

Bayan faruwar lamarin ne Shugaba Joe Biden ya bayyana a gaban manema labarai a mahaifarsa ta Delaware, inda yi Allah wadai da harin, yana cewa zai yi magana da abokin hamayyar nasa, domin taya shi alhini.

Ya ce “wannan na ɗaya daga cikin dalilan da suka sa wajibi ne mu haɗa kan ƙasar nan, ba za mu ci gaba da tafiya a haka ba, wannan yaƙin neman zaɓe ne da yake da ’yancin yi ba tare da kowacce irin matsala ba.”

Daga baya Fadar White House ta tabbatar da cewa Mista Biden ya yi magana da Trump ta waya.

Su ma tsofaffin shugabannin ƙasar biyu, Barack Obama da George Bush, sun bayyana jin daɗinsu da cewa Mista Trump bai ji rauni sosai ba.

Tuni su ma ’yan siyasa daga jam’iyyar tsohon shugaban ƙasar Trump ta Republican har ma da abokan hamayyarsa na Democrats suka fara yin tir da harin, suna kuma addu’ar samun sauƙi da nuna goyon baya ga tsohon shugaban.

Da yake miƙa saƙon jajensa a madadin Ƙungiyar Tarayyar Turai, shugaban Diflomasiyyar Turai Joseoh Borell ya yi Allah wadai da harin.

Shi ma a nasa ɓangaren sabon Firaiministan Birtaniya Keir Starmer ya ce wannan abu ne mai firgitarwa da bai kamata a ce ya faru ba.

Haka abin yake ga shugaban Hungary Viktor Orban, da kuma Firaiministar Italiya Giorgia Meloni.

Firaiministan Isra’ila Benjamin Natenyahu da mai daƙinsa Sara cikin kaɗuwa sun miƙa saƙon jaje ga shugaban, tare da fatan cewa zai sami sauƙi cikin gaggawa.

Shugaban Argentina Javier Milei, a nasa ɓangaren ya ce abin kunya ne a riƙa samun fitar irin wannan labari daga Amurka.

Shi kuwa shugaban Brazil Lula da Silva ta cikin sanarwar da gwamnatinsa ta fitar ta yi wa shugaba Trump fatan samun sauƙi cikin gaggawa.

Gwamnatocin ƙasashe Costa Rica, da Chile da Bolivia duk sun aike da saƙon su na jaje.

Ta cikin saƙon da ya fitar, Firaiministan India Narendra Modi ya ce yana cikin damuwa a sakamakon halin da abokinsa ya tsinci kansa.

Daga ɓangaren Fumio Kishida Firaiministan Japan ya ce ya zama dole ƙasashen duniya su haɗa hannu don yaƙi da harin da ake kaiwa ’yan siyasa kawai saboda saɓanin jam’iyya.

A nasa ɓangaren Shugaban Taiwan Lai Ching-te, bayan miƙa saƙon jajensa ga Trump, ya kuma miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan mutumin da ya rasa ransa a wajen da lamarin ya faru.

Shi ma shugaban Australia Anthony Albanese ya ce wannan al’amari ne mai ban tsoro, yana mai fatan cewa shugaban zai sami sauƙi cikin gagawa.

A nasa ɓangaren Firaiministan New Zealand Chris Luxon ya ce lokaci ya yi da ya kamata a kawo ƙarshen tashin hankali a lokutan siyasa.