An samar da babura 15 domin inganta tsaro a Jami’ar Ahmadu Bello

Hakan ya kara fito da yadda aka bai wa fannin tsaro muhimmanci a dukkan rassan jami’ar.

An samar da babura 15 domin inganta tsaro a Jami’ar Ahmadu Bello

Baburan da aka samar domin inganta ayyukan tsaro a Jami’ar Ahmadu Bello

Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta samar da sabbin babura 15 ga sashin tsaro na jami’ar domin inganta ayyuka a dukkan tsangayoyinta.

Da yake kaddamar da baburan, Shugaban Jami’ar, Farfesa Kabiru Bala ya ce samar da baburan na daga cikin kokarin da jami’ar ke yi na inganta harkar tsaro domin kare rayuka da dukiyar ma’aikata da dalibai da kuma al’umomin da ke makwabtaka da jami’ar.

Sanarwar da sashin hulda da jama’a na jami’ar ya fitar, ta bayyana cewar Farfesa Kabiru Bala wanda ya sami wakilcin mai rikon shugabancin tsaro na jami’ar Malam Ashiru T. Zango ya ce baburan za su taimaka wajen samar da tsaro musamman a harabobin jami’ar.

Farfesa Bala ya bukaci sashin tsaron da su tabbatar sun yi amfani da baburan tare da kulawa da su yadda ya kamata domin a cimma manufar samar da su.

Tun da farko a jawabinsa, Malam Ashiru Zango ya yi godiya ga mahukntan jami’ar bisa samar da baburan duk da rashin kudi da jami’ar ke fuskanta a halin yanzu.

Ashiru Zango ya tabbatar da cewa za su yi amfani da baburan kamar yadda ya kamata domin cimma manufar samar da su.

Shugaban tsaron ya ce wannan yunkuri ya kara fito da yadda aka bai wa fannin tsaro muhimmanci a dukkan rassan jami’ar da ke Kongo da Funtuwa da Gidan Arewa da kuma Samaru.

Isra’ila ta sake fitar da sabon sharaɗin tsagaita wuta a Gaza

Mutanen da gobarar tankar mai ta kashe sun kai 86 a Neja

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja