An samar da dandalin zumunta da ya haramta batsa
Wata kungiyar masu wa’azin Kirista a kasar Brazil ta kaddamar da wani shafin sada zumunta na zamani wanda za a rika yin rantsuwa ba za a yi batsa a cikinsa ba kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana. kungiyar, mai suna Facegloria, ta yi ikirarin cewa tun da aka kaddamar da shi a […]
Wata kungiyar masu wa’azin Kirista a kasar Brazil ta kaddamar da wani shafin sada zumunta na zamani wanda za a rika yin rantsuwa ba za a yi batsa a cikinsa ba kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.
kungiyar, mai suna Facegloria, ta yi ikirarin cewa tun da aka kaddamar da shi a watan jiya, shafin ya samu mambobi guda dubu 100.
kungiyar ta haramta yin amfani da kalmomi 600 a shafin, sannan akwai wani madanni mai suna “Amin” wanda mutum zai latsa idan yana so ya yaba kan wani abu da ya burge shi a dandalin.
Ko a shekarar 2013 ma, wata kungiyar Musulmai mai suna Ummaland ta kaddamar da irin wannan dandali, inda a yanzu take da mambobi kusan dubu 329.
Wasu daga cikin abubuwan da ta ware su ne “Wani gurbi da ba zai ba da dama a rika ganin abubuwan da mata ke wallafawa, da kuma kuma wallafa jawabai na fadakar da mutane.
Wasu daga cikin mutanen da suka kaddamar da shafukan, Maruf Yusupob da Jamoliddin Daliyeb sun ce “Mun samar dandalin sada zumunta na Ummaland bisa tsarin addinin Musulunci: babu gulma, ko cin naman mutane; muna mayar da hankali ne kan abubuwan da suka dace”.
Shi dai dandalin sada zumunta na Facegloria ana yin amfani da harshen Portuguese ne wajen sadarwa, amma ana sa ran za a fara amfani da wasu harsunan nan gaba kadan.
Kasar Brazil ce ke da mafi yawan mabiya darikar Roman Katolika a duniya.
Atilla Barros ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na AFP cewa “Za ka ga hotunan tayar da hankali da na batsa a Facebook.Hakan ne ya sa muka kudiri aniyyar samar da dandalin sada zumuta a shafin intanet domin isar da sakonni game da addini da abubuwan da Allah ya ke cewa.”
Hakazalika, an haramta watsa hotunan masu auren jinsi guda a dandalin.
Lauyoyi suna yajin aiki a Ghana
Fiye da lauyoyi 150 daga dukkanin jihohin kasar Ghana sun fara yajin aiki shekaran jiya Laraba.
Lauyoyin na yajin aikin ne domin su matsa lamba kan gwamnati ta kara musu albashi, sannan ta sanya su a cikin tsarin karbar fansho.
Yajin aikin zai kawo tsaiko a kan shari’ar manyan laifuka da ake gudanarwa a kasar.
Shakka babu yajin aikin zai jawo cikas ga fanin shari’ar kasar. Hakazalika, a kwanakin baya ne ma’aikatan fannin shari’a suka shiga yajin aiki a kasar.
kasar Ghana na fama da matsalolin tabarbarewar tattalin arziki, lamarin da ya sa take daukar matakan tsuke-bakin-aljihu.