An samar da dokar bai wa Mata ‘yancin cin gado a Abiya
Mata ’yan kasa ne da ke da hakki daidai da na maza.
Gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu, ya sanya hannu kan kudirin dokar da ta bai wa mata ‘yancin cin gado, da kuma mallakar kadarorin da mahaifansu suka mutu suka bari.
A makonnin da suka gabata ne dai Majaliar Dokokin Jihar ta zartas da kudurin, a kokarinta na samar wa jihar dokokin da za su yi gogayya da na sauran kasashen duniya.
- Yarima William da Kate sun ziyarci Amurka karon farko cikin shekaru takwas
- An cafke mahaifiyar da ta yi wa jaririnta yankan rago
Majalisar ta ce ta dauki wannan azama ce don kawar da duk wani nau’i na nuna wariya ga mata da al’ummar jihar ke yi a baya.
Da yake sanya hannun sa kan kudirin, Gwamna Ikpeazu ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki da hankali wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta, musamman ma a bangaren girmama mata, kasancewarsu halastattun ’yan kasa da ke da hakki daidai da na maza.
Haka kuma ya ce wannan sabuwar dokar, ita ce mafi muhimmanci da Majalisar Dokokin ta taba zartaswa a jihar, tare da yaba musu a bisa hakan.