An samar da gidan namun daji na tafi-da-gidanka a Saudiyya

Wani katafaren kantin sayar da kaya na Bawabat da ke birnin Abha ta kasar Saudiyya ya bude gidan kallon namun daji na tafi-da-gidanka. Wannan gidan kallon namun daji, ya mamaye fili mai fadin sukwaya mita dubu 30.Wannan kantin mallakar wani kamfani ne na Bawabat Al-Shorouk da ke kan titin Khamis Mushaiyt.Babban jami’in kula dakantin, Mansour […]

An samar da gidan namun daji na tafi-da-gidanka a Saudiyya
An samar da gidan namun daji na tafi-da-gidanka a Saudiyya

Wani katafaren kantin sayar da kaya na Bawabat da ke birnin Abha ta kasar Saudiyya ya bude gidan kallon namun daji na tafi-da-gidanka. Wannan gidan kallon namun daji, ya mamaye fili mai fadin sukwaya mita dubu 30.
Wannan kantin mallakar wani kamfani ne na Bawabat Al-Shorouk da ke kan titin Khamis Mushaiyt.
Babban jami’in kula dakantin, Mansour Al-kammash, ya bayyana cewa suna gudanar da bukukuwa na tsawon wata uku don nisahadantar da masu kawo ziyara, kuma suna sa ran samar da katafaren gidan kallon namun dajin tafi-da-gidanka a daukacin fadin Gabas ta tsakiya.
Wannan gidan namun daji ya samar da zakuna da nau’ukan damisa da birai da karnukan farauta da kuraye da kadoji da sauran dabbobi wadanda suka hada da macizai da yanyawa.
Ya ce masu ziyara za su nishadantu da kallon namun daji, inda wani mai wasa da dabbobin, Abu Jarrah, wanda ya shahara a daukacin fadin Gabas ta tsakiya zai rika nishadantar da su.

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF

Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana

An horar da mutum 500 dabarun adana ruwa don inganta muhalli a Gombe