An samar da karin mazabu a kananan hukumomi 10 a Jigawa
An samar da karin mazabu guda goma a Jahar Jigawa domin tinkarar zabuka masu zuwa da za ayi a shekarar 2019 a kasa baki daya. Jawabin hakan ya fito ne daga bakin baturen zabe na jahar dake wakiltar hukumar zabe ta kasa, Farfesa Riskuwa A Shehu a wani taro da hukumar ta yi a ranar […]

An samar da karin mazabu guda goma a Jahar Jigawa domin tinkarar zabuka masu zuwa da za ayi a shekarar 2019 a kasa baki daya. Jawabin hakan ya fito ne daga bakin baturen zabe na jahar dake wakiltar hukumar zabe ta kasa, Farfesa Riskuwa A Shehu a wani taro da hukumar ta yi a ranar Talatar da ta gabata, a dakin taro na hukumar zabe mai zaman kanta ta Jahar Jigawa.
Farfesa Riskuwa ya ce kananan hukumomin da abin ya shafa wajen samun karin cibiyoyin zaben, sun hada da karamar Hukumar Birniwa da aka kara wa mazabar Diginsa sai kuma karamar Hukumar Kaugama da aka kara wa mazabar Jarkasa, sai karamar Hukumar Kirikasamma da aka kara mata Baturiya.
Sauran sun hada da karamar Hukumar Garki da aka kara mata mazabar Maku, yayin da kuma Kazaure aka kara mata mazabar Dandi, sai karamar Hukumar Maigatari da aka kara wa mazabar Balarabe, yayin da karamar Hukumar Ringim ta samu krin mazabar Dabi.
Haka zalika karamar Hukumar Birnin Kudu aka ba ta mazabar Wurno, sai karamar Hukumar Gwaram da aka kara wa Basirka, ta karshe kuma karamar Hukumar Jahun aka kara mata mazabar Aujara. Da yake karin bayani jim kadan bayan an bayyana sunayen karin mazabun ga manema labarai da sauran ‘yan siyasa.
Farfesa Riskuwa ya ja kunnen ‘yan siyasa da su fadakar da magoya bayansu da su hanzarta wajen yankar katin zabe domin ganin sun tinkari zaben 2019 a daukacin zabukan da za ayi anan gaba idan Allah Ya kai mu.