An samar da takin zamani daga itacen darbejiya a Najeriya
Wani Kamfani daga Jihar Kebbi ya samar da takin zamani daga fahasar sarrafa ‘ya’yan itacen darbejiya wato (Neem) don habaka shuka tare da martaba fasahar cikin gida Najeriya don rage yawan dogaro da kayakin kasashen waje. Wannan samfurin takin dai an baje kolinsa ne a yayin gudanar da bikin nuna amfanin gona na bana a […]
Wani Kamfani daga Jihar Kebbi ya samar da takin zamani daga fahasar sarrafa ‘ya’yan itacen darbejiya wato (Neem) don habaka shuka tare da martaba fasahar cikin gida Najeriya don rage yawan dogaro da kayakin kasashen waje.
Wannan samfurin takin dai an baje kolinsa ne a yayin gudanar da bikin nuna amfanin gona na bana a Jihar Nasarawa a makon jiya. Haka zalika kamfanin bai tsaya nan ba, ya kuma samar da wani samfurin abincin dabbobi daga itaciyar ta darbejiya, da irin shuka na itaciyar mai inganci, da man girki daga itaciyar sannan da kuma maganin feshi.
Babban Daraktan Kamfanin, Alhaji Musa Karaye ya tabbatar da cewa wannan sabon samfurin takin zamani da kamfanin ya samar, yana saurin tsiradda amfanin gona yadda ya kamata, sannan kuma tasirinsa na jimawa a kasar da aka watsa shi tsawon lokaci.
Haka kuma ya ce a bisa jadawalin alfanun takin kamar yadda muka bayyana a cikin littafin yadda ake amfani da takin, ya nuna cewa takin na dauke da dukkan sinadaran da aka san takin zamani mai inganci na duniya ke dauke da su da suka hada da sinadaran nitrogen da phosphorus da potassium da zinc da manganese da kuma copper.
Bugu da kari Babban Daraktan ya ce kamfanin ya samu nasarar yin rajista a karkashin shirin bukasa amfanin gona na gwamnatin tarayya (GES) sannan sun amince da saida wa manoma samfurin saboda ingancincinsa don ciyar da harkokin noma gaba a kasar nan.