An same shi da rai bayan rijiya ta ribta da shi da awa hudu
Wani dalibi dan kimanin shekaru 22 ya ketare rijiya da baya cikin makon da ya gabata bayan rijiya ta abka masa, inda ya share tsawon awoyi hudu kafin a tono shi da rai, bayan mutane sun yi ta muhawarar a yi masa sallah a cike rijiyar saboda fitar da tsammanin za a iya samunsa da […]

Wani dalibi dan kimanin shekaru 22 ya ketare rijiya da baya cikin makon da ya gabata bayan rijiya ta abka masa, inda ya share tsawon awoyi hudu kafin a tono shi da rai, bayan mutane sun yi ta muhawarar a yi masa sallah a cike rijiyar saboda fitar da tsammanin za a iya samunsa da rai.
Shi dai wannan mutum mai suna Baba Habu Abubakar dalibi ne a kwalejin kimiyya da fasaha na Tatari Ali, inda yake shekarar farko na karatun diploma, al’amarin ya faru das hi ne a lokacin da wayar salularsa ta fada cikin rijiyar bayan ya dawo daga sallar la’asar, sai ya nemi izinin masu gidan domin ya shiga rijiyar mai zurfin gaba biyar domin ya fito da wayar, mai gidan ya amince masa, inda ya shiga ya yi lalube a cikin ruwan ya fito da wayarsa ya sanya cikin aljihu ya yi kokarin fitowa waje. Har ya kawo bakin rijiyar sai ginin bakin rijiyar da yake rike da bangarorinsa biyu suka balle inda ya fada cikin rijiyar, bulolukan da ya rike su ma suka bi shi, sannan kasar gefen rijiyar ita ma ta bi ginin suka rufta suka rufe shi na tsawon kusan awoyi hudu kafin aka tono shi.
Wakilinmu ya ziyarci unguwar Zango Federal Lowcost inda ya zanta da Abdullahi Adamu Sarkin Dawakin Sarkin Zango wanda suke tare da Baba Abubakar a lokacin da abin ya faru, ya ce a lokacin da suka duba rijiyar babu wanda zai ce akwai mutum a cikin rijiyar, saboda hatta ‘yan kwana-kwana da suka zo sai suka ce babu abin da da za su yi, illa a ci gaba da tono kurum, don haka suka taru da jama’a, wadansu na cewa ai sai a bari kurum a sallace shi saboda yanayin zurfin rijiyar, amma matasa abokansa suka ce tun da tona rijiyar aka yi dole sai sun sake tona ta sun ga yadda lamarin zai kasance, ko da gawarsa a fito da ita a ba iyayensa. Tun karfe hudu da minti sha biyar na yamma har kusan karfe takwas na dare ana tono har aka yi mangariba da isha, inda daga bisani aka tarar da hannunsa yana motsi a cikin kasa, aka bi aikin a hankali aka fito da shi, bai ji rauni ba, sai kujewa da ya yi a kansa da gadon bayansa.
Wakilinmu ya zanta da Baba Abubakar, wanda wannan waki’a ta abka masa, inda ya ce wayarsa ce ta fada rijiyar, sai ya ga zai iya shiga ya fito da ita, yayin da yake fitowa sai ginin rijiyar ya rubza a hannunsa suka abka tare, amma da Allah Ya taimake shi ya isa cikin ruwa ya fadi sai ginin ya giciye ya tokare gefe da gefen rijiyar, ya ga duhu, sai buraguzai da kasa da suka kange shi ta kowane gefe, idan ya shafa sai ya ji tubalan rijiyar a samansa kamar kabari. Da yake hankalinsa bai fita ba ya yi ta kiran neman taimako amma ya fahimci babu wanda ke jinsa, shi ma ba ya jin komai, har tsawon sama da awoyi uku, yayin da zafi ya fara damunsa, ya san cewa ya shiga cikin mawuyacin hali sai inda Allah ya yi da shi. Daga wannan lokaci ya ce har ya sadakar, sai ya fara jin kasa tana sake zuba kansa tana danne shi, sai ya fahimci cewa ana tone rijiyar ce, don haka ya fara magana yana cewa su rika takawa a hankali, sai ya yi ta tura hannunsa sama har aka gani aka tona a hankali aka zakulo shi, aka kai shi asibiti.
Ya ce, bude shi ke da wuya sai ya ji wata iska mai dadi ta buge shi, alhali kafin wannan lokacin har ya fara jin numfashi na dauke masa saboda zafi.
Baba Abu ya ci gaba da cewa, a lokacin da ya fara jin maganar mutane sai ya ji dadi ya gode wa Allah, saboda ya fahimci da sauran shan ruwansa, don haka a lokacin da aka fito da shi har aka kai shi asibiti, sai yana ganin abin kamar mafarki ne, daga nan aka sanya masa magani a raunukan da ya yi, ko minti talatin bai yi ba a asibitin aka sallame shi ya dawo gida.
Ya ce zai ci gaba da sana’arsa ta kafinta da karatunsa kuma ba zai sake gangancin shiga rijiya ba matukar ba daya ne daga cikin mahaifansa suka fada suka nemi taimakonsa ya ga zai iya taimakawa ba.
Wani Limami a unguwar da al’amarin ya faru Ustaz Hassan Usman Zango ya bayyana cewa, wannan aya ce Allah Ya nuna wa mutane, da kuma ishara na a kadaita Allah, a kuma daina saurin zartar da hukunci kan rayuwa wacce ta Allah ce, a duk halin da aka tsinci kai a ciki. Don haka ya shawarci mutane su rika kadaita Ubangiji su kuma kara tsarkake imaninsu, su sani Shi ne mai kashewa, Shi ne kuma ke rayawa. Musamman ganin wannan mutum ya rayu kusan sa’a hudu a cikin rijiya a karkashin kasa, amma aka kai shi asibiti ba tare da bata lokaci ba aka sanya masa magani a raunukan da ya samu ya dawo da kafafunsa. Wannan abin mamaki ne.