An sami dan tayi mai siffofin dabbobi biyar a mahaifar tunkiya

Mahautan da ke sana’ar fawa a kasuwar Alaba da ke Legas sun ga abin al’ajabi yayin da suka sami dan tayi mai siffofi iri-iri a cikin wata tunkiya da suka fede.daya daga cikin mahautan da suka fede tunkiyar, Shu’aibu Haruna ya bayyana wa Aminiya cewa siffofin dan tayin sun ba su mamaki. “Lokacin da muka […]

An sami dan tayi mai siffofin dabbobi biyar a mahaifar tunkiya

Daga dama, dantayin ne mai siffofin dabbobi biyar, bakinsa ya yi kama da na mage, kunnuwansa kamar na zomo, ga shi kuma da dagi irin na kare. Allah daya, gari banban.Mahautan da ke sana’ar fawa a kasuwar Alaba da ke Legas sun ga abin al’ajabi yayin da suka sami dan tayi mai siffofi iri-iri a cikin wata tunkiya da suka fede.
daya daga cikin mahautan da suka fede tunkiyar, Shu’aibu Haruna ya bayyana wa Aminiya cewa siffofin dan tayin sun ba su mamaki. “Lokacin da muka fede ta, sai muka ga ’yan tayi biyu a cikinta. daya lafiyarsa kalau, kamaninsa irin na tunkiya sak, dayan kuma rabinsa kamar tunkiya, rabinsa kuma kamar kare kuma ya yi kama da alade, idonsa irin na kyanwa, sannan kuma kunnensa ya yi kama da na zomo. Wuyansa a hade yake, bai fito kamar na tunkiya ba. Wani abin mamaki an kammala halittarsa, haihuwarsa za a yi amma Allah bai ba tunkiyar iko ba”.
Ya ci gaba da cewa, “Muna ganin saboda tayin mai siffofi biyar ya toshe hanyar mahaifar, ya sa dayan bai fito ba. Mun lura cikinta yana da girma, kuma da alamun mai ita ya yi mata sakiya a cikin, kila yana zaton wani ciwo take da shi a cikin nata”.
Malam Shu’aibu, dan asalin karamar Hukumar Munjibir a Jihar Kano ya bayyana cewa tun da yake sana’ar fawa shekaru fiye da talatin da biyar da suka gabata a kasuwar bai taba ganin dabba mai siffar dan tayin ba.
Sai dai ya bayyana cewa shekaru da dama da suka gabata sun taba samun akuyar da aka rubuta sunan Allah a hantarta da wata da aka rubuta lambobi a huhunta.
Malamai da dama da Aminiya ta tuntuba, sun bayyana cewa babu abin mamaki a sami wata dabba mai siffofi da yawa, domin Allah Yana iya yin duk abin da Ya so don Ya nuna ikonSa.
Wani likitan dabbobi, mai suna Dokta Michel Dare ya bayyana cewa ba kasafai ake samun irin haka ba, sai dai in barbara aka yi da wata dabbar daban.