An sami rahoton saran maciji sama da 700 a asibiti daya a Binuwai
Asibitin dai ya yi fice wajen duba marasa lafiyan da maciji ya sara.
Sama da mutane 700 ne daga sassa daban-daban na jihar Binuwai suka fuskanci saran maciji a cikin shekarar 2020 kuma suka sami kulawa daga Asibitin Tunawa da Bishop Murray dake Makurdi, babban birnin jihar.
Babban Jami’in Cocin Katolika dake Makurdi dake kula da asibitin, Rabaran Fada Peter Kpaleve ne ya tabbatar da hakan ranar Litinin loacin da ya karbi bakuncin Gwamnan jihar Samuel Ortom.
Gwamnan dai ya ziyarci asibitin ne domin duba yanayin da wadanda rikicin makiyaya da manoma ya ritsa da su a yankin.
Rabaran Kpaleve ya ce asibitin nasu ya yi fice wajen duba marasa lafiyan da maciji ya sara, ko da yake ba iya wadanda suke dubawa kenan kawai ba.
A cewarsa, “Yau Gwamna ya zo saboda jajircewar Gwamnan ce ta sa babu wanda ya zo asibitin nan a bara sakamakon saran maciji kuma ya rasa ransa daga cikin sama da 700.
“Kula da kuma jinyar wadanda maciji ya sara abu ne mai matukar tsada, kuma galibi wadanda lamarin ya fi shafa masu karamin karfi ne da ba za su iya biya ba.
“Amma dukkansu sun sami kulawa sakamakon tallafin Gwamna Ortom. Hakan ne ya sa asibitinmu ya kasance daya daga cikin mafiya inganci a jihar Binuwai,” inji shi.
Da yake nasa jawabin, Gwamna Ortom ya jinjinawa asibitin kan irin rawar da yake takawa wajen inganta harkar lafiya a jihar.
Ya ce gwamnati ta fara hadin gwiwa da asibitin ne tun kusan shekara ta 2000 lokacin da ta gano cewa yana da kwarewa da kuma kayan aikin kula da wadanda macijin ya sara.
“Saran maciji na da matukar hatsari, kuma a mafi yawan lokuta, ikon Allah ne kawai yake sa wa a warke daga shi.”
Gwamnan ya kuma kara da cewa a yanzu haka akwai kusan basussukan Naira miliyan 70 da ake bin gwamnatinsu bashi amma asibitocin suka ci gaba da kula da marasa lafiyan.