An sami sa da ragon da suka fi tsada a Legas
A yayin da bikin Kirsimeti ke kara karatowa, farashin dabbobi sai kara hauhawa yake yi, inda a lokacin rubuta wannan rahoto, aka sami san da ya kai fiye da Naira miliyan daya da rago na Naira dubu dari biyar a kasuwar Alaba Rago da ke Legas.Dillalin san, mai suna Usaini Mairago Alaba ya shaida wa […]

A yayin da bikin Kirsimeti ke kara karatowa, farashin dabbobi sai kara hauhawa yake yi, inda a lokacin rubuta wannan rahoto, aka sami san da ya kai fiye da Naira miliyan daya da rago na Naira dubu dari biyar a kasuwar Alaba Rago da ke Legas.
Dillalin san, mai suna Usaini Mairago Alaba ya shaida wa Aminiya cewa an kawo san daga kasar Holand. “An kawo su ne guda biyu, aka sayar da babban a kan Naira miliyan daya da dubu dari biyu, mai yiwuwa saboda ba dan kasa ba ne. Abin da ya bambanta shi da sauran shanu shi ne yawan nama da tsawo. Gaskiya ban taba jin sa mai kudin wannan ba a cikin kimanin shekara 35 da nake harkar sayar da dabbobi a kasuwar Alaba. A kasuwarmu ba mu da san da ya wuce Naira dubu dari hudu zuwa dari biyar. Shi wannan sa ya fi namu cin abinci. Saboda yana shan garwar ruwa takwas zuwa goma a rana. Kuma yana cin abinci da yawa fiye da namu dabbobin”. Inji shi.
Shi ma dillalin raguna a kasuwar Alaba mai suna Baba Miko Mairago ya ce, “An taya ragon da ake yi masa lakabi da Fari, a kan Naira dubu dari hudu, amma ba a sallama ba, saboda ana ganin zai kai Naira dubu dari biyar. Bambancinsa da sauran raguna shi ne girmansa da farinsa da tsawonsa da kuma alamun yawan namansa. Ina tabbatar maka da cewa idan kirsimeti ta zo, zai iya fin haka. Akwai mai biye masa mai suna Gamboru Buzu da kudinsa ya kai Naira dubu dari hudu zuwa da hamsin”.
Sarkin kasuwar Alaba Rago, Alhaji Umaru na Goggo Sakkwato ya tabbatar da labarin, inda ya ce dalilin da ya sa san ya yi tsada sosai shi ne saboda girmansa da kuma kasar da aka zo da shi. “Gaskiya san ya ba mu mamaki sosai, saboda girmansa da alamar yawan namansa. Ban taba ganin sa mai girman irin wannan ba, a nan kasuwar Alaba. Ka san da irin su kamfanoni ke yin madara da muke sha”. Inji shi
Mahauta da dillalan dabbobi da Aminiya ta tuntuba a sassa da dama na Legas sun bayyana cewa ba su taba ganin san da ya kai Naira miliyan daya ba a rayuwarsu.
Shugaban kungiyar mahauta ta United Butchers Association (UBA) da ke kasuwar abbatuwa ta Agege, Alhaji Umar Adam ya ce, “Gaskiya ban taba ganin san da ya kai Naira miliyan daya ba, amma na taba jin ragon da aka ce an saya Naira miliyan a shekarun baya”.