An sami wata atamfa dauke da kamar shahada a Legas

An sami wata atamfa dauke da kalmar shahada baro-baro da aka rubuta da Larabci a jikinta.Wani kamfanin yin atampa na Ultimate Dabiba ne ya fitar da zayyanar rubutun ‘La’ilaha Illallahu Muhammadur Rasulullah’, a atamfar mai launin bula, wacce aka saya a shagon wata mata da ke kasuwar Oshodi a Jihar Lagos.Malam Muhammadu Abdulhamid, shugaban makarantar […]

An sami wata atamfa dauke da kamar shahada a Legas

An sami wata atamfa dauke da kalmar shahada baro-baro da aka rubuta da Larabci a jikinta.
Wani kamfanin yin atampa na Ultimate Dabiba ne ya fitar da zayyanar rubutun ‘La’ilaha Illallahu Muhammadur Rasulullah’, a atamfar mai launin bula, wacce aka saya a shagon wata mata da ke kasuwar Oshodi a Jihar Lagos.
Malam Muhammadu Abdulhamid, shugaban makarantar Islamiyya ta Ardus Salam da ke Agege, wanda ya  adana atamfar, ya bayyana cewa wata dalibarsa ce ta fara ganin atamfar bayan wata kawarta ta sanar da ita.
Ya bukaci a kawo masa atamfar ya gani, sannan ya ce su bar masa ita domin ta zama wa’azi kuma abin misali ga jama’a. “Shi ya sa na ajiye ta don na rika fadakar da jama’a. Bai kamata mutum ya daura atamfar ba, domin sunan Allah da mazonSa da take dauke da shi. Hasali ma mutum yana iya fita daga Musulunci, muddin ya wulakanta ta ko kuma ya shiga da ita cikin najasa alhalin yana sane”.  Inji shi.
Mutane da dama da suka ga atamfar sun yi Allah-wadai da kamfanin da ya yi atamfar. Wasu da dama kuma sun bayyana cewa da gangan wasu kamfanoni ke yin irin atamfar don su bata wa musulmi rai ko kuma su tsokane su a  yi tashin hankali.
Shi dai kamfanin da ya yi atamfar, bai sanya adireshinsa a atamfar ba, ko kuma lambar waya da za a iya tuntubarsa. Ko yanar gizo ko kuma wata alama da ke nuna kasar da yake. Sai dai wasu sun bayyana cewa kamfanin na wata kasar waje ne da ke kiyayya da Musulunci.
An sahawarci ‘yan kasuwar da ke jihar ta Legas da saurana jihohi su daina mu’amala da kamfanin Dabiba saboda cin zarafin Musulunci da kamafanin yake yi.