An samu ƙaruwar rashin tsaro a Najeriya — Rahoto

Rahoton ya nuna ƙarin adadin da aka samu wanda ya yi sama idan aka kwatanta da watan Afrilu.

An samu ƙaruwar rashin tsaro a Najeriya — Rahoto

Wani rahoto da kamfanin Beacon Consulting ya fitar, ya nuna cewa an samu ƙaruwar matsalar tsaro a watan Mayun 2024 da kashi 10.28.

Rahoton ya ce an samu faruwar Hare-hare da ke nuna taɓarɓarewar tsaro sau 762, idan aka kwatanta ta watan Afrilu wanda al’amuran rashin tsaro suka faru sau 691.

“A Watan Mayu, 2024 ya gano yadda rashin tsaro ya ƙara ƙamari, inda ya ƙaru da kaso 262.70 saboda samun ƙaruwar garkuwa da mutane.

“Ana kuma alaƙanta hakan ne sakamakon hare-haren ‘yan bindiga a Arewa Maso Yammacin ƙasar (Najeriya)…” a cewar rahoton.

Amma rahoton ya nuna cewa duk da samun ƙarin matsalolin tsaro da aka samu a watan Mayu, amma kuma an samu ragin yawan mace-mace a watan, inda alƙaluman suka ragu zuwa 1090 daga 1097 a watan Afrilu.

Kazalika rahoton ya nuna raguwar mace-macen ne da kashi 0.64.

Rahoton ya kuma lissafa jihohin da aka fi samun matsalolin da suka haɗa da Borno da Edo da Abuja da Kaduna da Katsina da Kogi da Kwara da Neja da Sakkwato da kuma Jihar Zamfara.

Rahoton kamfanin ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su ɗauki matakan da suka dace wajen ganin an kare dukiya da rayukan al’umma.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos