An samu ambaliyar ruwa a Kamaru

Daminar bana ta haddasa ambaliyar ruwa a wasu sassan birnin Douala a kasar Kamaru. Hakan ya jawo asarar kayayyaki da sutura da abinci da sauransu.Har ila yau, ambaliyar ta ci ran wani yaro mai shekara biyu da haihuwa. Hukumomi a birnin Douala sun bayyana wannan ambaliya da rashin bin tsarin yin gini da jama’a suka […]

An samu ambaliyar ruwa a Kamaru
An samu ambaliyar ruwa a Kamaru

Daminar bana ta haddasa ambaliyar ruwa a wasu sassan birnin Douala a kasar Kamaru.
Hakan ya jawo asarar kayayyaki da sutura da abinci da sauransu.
Har ila yau, ambaliyar ta ci ran wani yaro mai shekara biyu da haihuwa. Hukumomi a birnin Douala sun bayyana wannan ambaliya da rashin bin tsarin yin gini da jama’a suka yi.
An ce galibinsu suna yin gini ne a hanyoyin magudanan ruwa, ko kuma suna yin gini a cikin fadama abin da dokar tsarin gini ba ta yarda da shi ba. Hakan ne yake sa idan ruwa ya tsananta, sai ya fara yin kutse dakunan jama’a, yana kuma cinye  motoci.
Hakazalika, shige da fice yana gagarar mutane. Hakan yakan sanya wadansu majiya karfi, su goya su a baya, idan an fice daga cikin ruwa an sauke su ya biya su kudi da ya kai Dalar Amurka guda.
A  wani mataki na rigakafi, hukumomi a birnin Douala sun dauki matakin rusa duk gidajen da aka ginasu a kan magudanun ruwa da kuma na cikin fadama. Daga bisani kuma za a aiwatar da aikin alkinta magudanun ruwa da kuma gina gadaje a wasu unguwanni da aka ga akwai bukatar yin haka.