An samu bullar cutar kyanda a Kano
Hukumomi sun tabbatar da bullar cutar kyanda a sassan Karamar Hukumar Birni.
Hukumomin Jihar Kano sun tabbatar da bullar cutar kyanda a wasu unguwanni da ke Karamar Hukumar Birni.
Ko’odinetan kula da lafiya matakin farko na karamar hukumar, Aliyu Jinjiri Kiru, ya bayyana cewa yankunan da aka samu bullar cutar kyanda sun hada da Sharada, Madatai, da kuma Gandun Albasa.
Ko’odieta ya bayyana cewa an samu rahoton bullar cutar kyanda da sauran cututtuka masu yaduwa ne a cibiyoyin kiwon lafiya da dama a karamar hukumar.
Jami’ar yada labaran yankin, Fatima Abdullahi ta ruwaito shi yana kira da da a dauki matakin gaggawa na shawo kan cutar da kuma hana yaduwarta.
- Mafitar Taddamar Gwamnan Kano Da Shugaban Hisbah
- Magidanta uku na taƙaddama kan kayan ‘ya’yan wata mata a Oyo
A nasa bangaren, jami’in kula da harkokin yaki da cututtuka, Tukur Hassan, ya ce tuni sun tura wadadan suka kamu da cututtukan zuwa Aasibitin Kwararru na Murtala domin killace su.
Sai dai bai bayyana hakikanin adadin wadanda suka kamu ba.
Hakimin Karamar Hukumar Birni, Madakin Kano, Alhaji Yusuf Nabahani, ya yi kira ga dukkan masu unguwanni da masu dagattai da su ba da fifiko kan harkokin kiwon lafiyar jama’a a kowanelokaci saboda muhimmancinsa.