An samu bullar Cutar Lassa a Gombe
Zazzabin Lassa ya kama wani matashi bayan mako biyu da dawowarsa daga Jihar Adamawa.
An samu bullar zazzabin Lassa yayin da aka tabbatar da samun cutar a jikin wani matashi dan shekara 25 a Jihar Gombe.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dokta Habu Dahiru ne ya bayyana hakan da cewa wannan shi ne karon farko da aka samu cutar bana a jihar.
- Dokar Najeriya ta haramta biyan kuɗin fansa — Ministan Tsaro
- Yadda saran maciji ya kwantar da mutum 2,700 a Gombe
Kwamishinan ya ce an samu cutar a jikin matashin ne wanda ya dawo daga balaguron da ya shafe makonni biyu a Jihar Adamawa
Dokta Habu ya ce da farko an soma kwantar da matashin a Asibitin Sunnah bayan zazzabi ya kama shi, amma daga bisani aka mayar da shi asibitin Ahajas, inda a nan ma lamarin ya faskara a garzaya da shi Asibitin Koyarwa kuma sakamakon gwaji ya tabbatar yana ɗauke da cutar ta Lassa.
Kwamishinan ya ce kamar yadda kowa ya sani ana samun cutar a jikin wasu irin beraye masu nonuwa da yawa a jikinsu a lokacin da suka samu abinci a bude suka sa baki ko suka yi kashi a ciki.
Ya ce daga cikin alamomin cutar akwai zazzabi mai zafi da mutuwar jiki da kasala wanda yakan sa a ko yaushe mutum ya ji jikinsa a mace babu karfi, ga kuma fitar jini ta baki ko ta mafitsara ko ta kunne.
Kwamishinan ya yi gargadin cewa idan har ba a yi gaggawar zuwa asibiti ba, cutar na iya zama sanadiyar mutuwar mutum.
Ya kara da cewa, idan zazzabin Lassa ya kama mace mai juna biyu zai iya halaka ta har ma da jaririn da ke cikinta.
Kazalika, ya bayyana cewa dama dai Jihar Gombe da Adamawa da Taraba da Benuwe da Kogi suna cikin jihohin da suke da hatsarin kamuwa da wannan cutar.
Ya ce biyo bayan samun wannan cutar Gwamnatin Jihar Gombe ta farfado da wata Cibiya a Ma’aikatar Lafiya da za ta riƙa ba da agajin gaggawa da kuma fadakar da al’umma a kan hanyoyin dakile yaduwarta.
Ya yi kira ga al’umma da su bqi wa jami’an lafiya hadin kai wajen zuwa asibitoci domin yin gwajin da zarar an ga alamun cutar saboda ɗaukar matakin da ya dace.
Haka kuma, ya ce an tanadi waje na musamman da za a riƙa kula da masu wannan cutar saboda hatsarin yaduwarta.
Ya bayyana cewa kawo yanzu dai cutar ba ta da rigakafi, saboda haka hanya mafi sauki na kare kai shi ne tsabtace muhalli.
Ya kuma ja hankalin jama’a da suke shanya masara a bakin titi da cewa su mayar da hankali saboda a nan ma berayen suna yawo a kai suna kashi da fitsari, wanda matuƙar ba a kula ba za a yi aikin da na sani.
“Tunda cutar ba ta da rigakafi idan ana son a rage ta dole a kula da tsabtar muhalli sannan wadanda suka kamu a gaggauta mai su Asibiti domin su samu kulawad da ta dace.”