An samu bullar Zazzabin Lassa a Abuja

Kawo yanzu mutum biyu ne suka kamu da cutar Zazzabin Lassa a Babban Birnin Tarayya.

An samu bullar Zazzabin Lassa a Abuja

An tabbatar da kamuwar mutum biyu da cutar Zazzabin Lassa a Babban Birnin Tarayya.

Sakatariyar Hukumar Lafiya ta birnin, Adedolapo Fasawe, ce ta sanar da haka a ranar Litinin, amma ta ce babu wanda cutar ta kashe a birnin.

Adedolapo Fasawe ta ce an gano masu dauke da kwayar cutar ce a Babban Asibitin Bwari da kuma Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja.

Cikin wadanda suka kamun har da wani dan watanni 14, wanda cutar ce sanadin rasuwar mahaifiyarsa a  Jihar Bauchi, kafin a dawo da shi Abuja.

An dawo da wutar lantarki a Kaduna

An kashe ɗan banga da yin garkuwa da ’yan mata 6 a Neja

’Yan fashin teku sun sace jirgin fasinja mutum 11 sun ɓace a Ribas

Jirgin Amurka ɗauke da mutum 10 ya ɓace

Tags