An samu canjin? (2)
A makon da ya wuce mun tsaya inda muke tambayar kanmu, me ke nan ya dace a ce yanzu ana yi ko za a iya yi domin kawo canji na hakika a cikin kasa, har kafin jagoran canjin ya hau karaga? Na san wasu suna da ra’ayin cewa ai matsalar kasar nan ta shugabanni ce, […]
A makon da ya wuce mun tsaya inda muke tambayar kanmu, me ke nan ya dace a ce yanzu ana yi ko za a iya yi domin kawo canji na hakika a cikin kasa, har kafin jagoran canjin ya hau karaga?
Na san wasu suna da ra’ayin cewa ai matsalar kasar nan ta shugabanni ce, da zarar aka ce Buhari ya hau; ’yan majalisar da aka zaba karkashin Jam’iyyar APC sun fara aiki; gwamnonin APC sun dare kan karagar mulki; Buhari kuma ya zabi ministoci da sauran jami’an gwamnati, nagari, to canji ya samu; ba don komai ba sai maganar azancin nan da Hausawa ke yi mai nuni da cewa kifi bai fara lalacewa, sai daga kai, ba daga wutsiya ba. Eh, hakan na iya zama gaskiya, amma kuma in mutum ya tsaya da kyau ya dubi lamurran kamar yadda suke, zai ga cewa, gyaran da muke bukata daga sama da kasa ya kamata ya kasance, tamkar yadda ruwan dufana ya yi nasa gyaran a zamanin Annabi Nuhu. Akwai hujjoji da dama da suke nuni da haka.
Mu fara da murnar cin zaben Buhari da aka yi kwanaki ana yi a yawancin fadin kasar nan da irin rasa rayukan da aka yi, tun daga ranar nake ganin cewa ba mu yi wa canjin nan adalci ba, balle shi wanda ya jagoranci canjin. Bai yiwuwa a ce saboda murnar mahaifiya ta haihu sai a shiga karkashe sauran ’yan uwan da ta haifa, a ce wannan ci gaba ne.
Ba wani abu ya fi tayar da hankali ba irin ganin cewa sai da Buhari ya fito fili ya yi kira ga mutane da a yi murnar cin zabe cikin natsuwa da kulawa, amma me muka yi? Mun kashe kawunanmu. Mun farfasa motocinmu da na iyayenmu. Mun rufe hanyoyin motoci da na kafa. Mun hana mutane sakat da gudu da babura da motoci. Mun kafa tunga da aka rika zagi da matsa wa yawancin wadanda suka wuce ta wurin. Duk saboda murna! Ina ga tunda farko ya dace mu nuna wa duniya cewa jiya ba yau ba ce. Idan kafin zabe mun kasance masu taurin kai da rashin jin magana, bai kamata bayan an samu canji mu ci gaba da wadannan irin miyagun halaye ba. Idan shugabanni sun ce mu bari, to, ya kamata mu hanu, ba wai mu yi kunnen-uwar- shegu ba. Gyaran a nan na wane ne?
A nan, ina ga iyaye da sauran al’umma su ne ya dace su fara maganar gyaran ba gwamnatin Buhari ba! Yaron da ya yi wauta da motar mahaifinsa, ko wadda mahaifinsa ya saya masa, aka kwararratsa ta, cikin murna da annushuwa, ya aika gida a turo wata motar, iyayensa ba su ce uffan ba, saboda canji ya samu, ina jin ba su yi wa Buhari ko canjin nan adalci ba! Tarbiyyar ’ya’ya da dukkan wadanda ke kusa da mu, ina jin alhakin farko na iyaye ne da sauran masu hurumin tarbiyyar a cikin al’umma. Idan da gaske mu ne muka yi amfani da makamin kawo canji na jefa kuri’a a lokacin, to ya dace a ce mun san abin da muke yi. A lokacin jefa kuri’a mun fita mun sha rana da kura da yunwa don kawo canji a kasa, amma mun kasa kawo canji a cikin gidajenmu da na makwabta, ina amfanin badi ba rai!
Ba wannan ba kadai, na ji da yawa daga cikinmu na ta fadar ai bari kawai cikin shekara hudu masu zuwa komai zai gyaru, ba dai an samu canjin ba, ai Buhari ba zai bar miyagun iri da munanan halaye su ci gaba da wanzuwa ba. Abin tambaya shi ne ba za mu samu canji a cikin lamurran rayuwarmu ba ke nan sai an yi shekara hudu na mulkin Buhari? Ba za mu kwabi ’ya’ya da wadanda Allah Ya dora mana alhakin kula da su ba, sai Buhari ya kama mulki, sai ya yi shekaru yana fama da mu, kamar wasu dabbobi? Ba wata rawa da za mu taka mu a matsayinmu na wadanda suka zabi canjin da wanda zai jagorance shi?
Idan canjin na Buhari ne kadai, to da alama mun yi wa harkar canjin shiga daki irin ta ’yan bori, da baya. Domin kuwa ba yadda canjin sama zai wakana, na kasa na jira, tafiya ya kamata su yi tare. Shi ya sa duk wani da ke tukin ganganci saboda Buhari ya ci zabe, ba canji ya zaba ba, sai dai wahala. Duk wani da zai rika bin kwararo yana zubar da shara, to da alama ya manta da canji, domin ba ya tare da shi. Duk wanda yake ajiye abin hawa haka nan barkatai ba bisa ka’ida ba a kan titi, shi ma ba ya tare da Buhari da canjin da muke ta hankoro. Duk wani da yake ci gaba da yin sata da cin hanci da babakere da dukiyar jama’a, a inda aka ba shi amana har yanzu, yana jira sai Buhari ya hau, ya bari ko in an yi doka ta sa dole ya bari, to wannan ma ba da gaske yake yi ba, ba canji yake so ba, domin kamata ya yi a ce tun ranar zaben Buhari irin wadannan mutane sun tuba, sun bi guguwar canji, ba wai sai ta zo ta wuce da su ba, su zo suna da-na-sani.
Ina mafita?
Mu shigar da canji a cikin rayuwarmu ta yau da kullum kafin Buhari ya hau. Ina matan aure, ban da almundahana da kudin cefane! Ina dalibai ’yan makaranta, ban da satar jarrabawa da makamantansu! Ina ma’aikatan hukuma, irin su ’yan sanda da kwastan da imigireshin da makamantansu, a ga canji wajen gudanar da ayyuka! Ina masu sayar da hatsi, ban da tauye mudu! Ina teloli, ban da cin yadi da rashin cika alkawari! Ina……. Abin da yawa ba sai na lissafa kowa da komai ba, amma mun dai gane. Canji daga jikinmu ya kamata ya somo, abin da Buhari zai yi shi ne ya kasance jagora zuwa ga matabbatar gaskiya, aljannar canji! Fakat!