An samu fahimta tsakanin Fulani da al’ummar Kurmi(2)

Shuwagabannin kungiyar Fulani makiyaya ta Myyati Allah sun yi  rangadin gani da ido a jihohin Kudu maso yamma, zagayen da suka ce sun yi ne da yawun mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad II da daukacin sarakunan gargajiya na Arewa.kungiyar ta shirya ziyarar gani da idon ne domin kawo karshen kiki-kakan da ya taso tun […]

An samu fahimta tsakanin Fulani da al’ummar Kurmi(2)
An samu fahimta tsakanin Fulani da al’ummar Kurmi(2)

Shuwagabannin kungiyar Fulani makiyaya ta Myyati Allah sun yi  rangadin gani da ido a jihohin Kudu maso yamma, zagayen da suka ce sun yi ne da yawun mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad II da daukacin sarakunan gargajiya na Arewa.
kungiyar ta shirya ziyarar gani da idon ne domin kawo karshen kiki-kakan da ya taso tun bayan garkuwar da aka yi da Cif Olu falae da ma kara dankon zumuncin da ke tsakanin ’yan Arewa da abokan zamansu a Kurmi.  Rangadin ya gudana ne a makon jiya a karkashin jagoranci shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Muhammadu Juba, Ardon Zuru da mataimakinsa, Alhaji Usaini Baso da sakaterensa, Alhaji Usaman Baba Ngazarma da sauran gaggan shuwagabannin Fulani, a inda suka kai ziyarar gani da ido a jihohin Kwara da Oyo da Ogun da Legas kana suka hade jihohin Osun da Ekiti da Ondo, inda suka yi nasu taron a Akure, wurin da aka yi garkuwa da Cif Falae.
A taron kungiyar na Jihar Legas, shugaba Alhaji Abdullahi Lailaga ya yi kira ga Fulanin da su hada kansu, su guji kirkirar kananan kungiyoyin da ba za su kai su ko’ina ba, domin a cewarsa duk wannan fadi-tashin da ake yi saboda su ne; domin a kwato masu ’yanci, don haka su guji rarraba kawunansu, suna yi wa kungiyar kishiyoyi.
Shi kuwa shugaba  Alhaji Muhammadu Juba shaida wa Aminiya ya yi cewa, rangadin ba na Fulani kawai ba ne na, daukacin ’yan Arewa mazauna Kurmi ne, domin a yanzu sun kammala da Kudu maso yammancin Najeriya, sauran Kudu maso gabas da Kudu maso kudu; ya kuma kara da cewa  a ziyarar gani da idon, kwalliya ta biya kudin sabulu. Domin sun samu ganawa da shuwagabannin Fulanin yankin da na Yarabawa, da ma manyan jami’an tsaro na yankin kaf din su. “Mun kuma samu fahimtar juna da su.  Shi ma Cif Olu Falae ya nemi afuwarmu na rashin ganawa da shi ido-da-ido, domin a lokacin ba ya nan, ya tafi Abuja amma ya ba mu lokaci, za mu dawo mu tattauna da shi. Mun sami ganawa da basarake mai daraja ta daya a Akure, wato Deji na Akure Aladetoyinbo; wanda ya shaida mana cewa komi ya wuce, domin an samu fahimtar juna. korafin da ya yi mana kawai shi ne na matsalar makiyaya, wajen barnata amfanin gonar manoma mun kuma ja kunnen makiyayan kwarai da gaske.” Inji shugaban.