An samu gada mai dogon hancin da ke rufe bakinta
Wani kwararren masanin halittu mai suna Mista Trolle, ya kai mako guda a gabar ruwan kasar Rasha don daukar hoton wani jinsin dabbar gada da take rayuwa a Tsakiyar Nahiyar Asiya, inda take da dogon hanci da ya banbanta ta da sauran nau’o’in gada da aka saba gani. Wannan gadar dai hancinta ya rufe bakinta, […]
Wani kwararren masanin halittu mai suna Mista Trolle, ya kai mako guda a gabar ruwan kasar Rasha don daukar hoton wani jinsin dabbar gada da take rayuwa a Tsakiyar Nahiyar Asiya, inda take da dogon hanci da ya banbanta ta da sauran nau’o’in gada da aka saba gani.
Wannan gadar dai hancinta ya rufe bakinta, wanda hakan na hana kura shiga cikin huhunta lokacin hunturu.
Mista Trolle, dan kasar Demark ya kai sama da shekara 25 yana nazarin jinsin halittun dabbobi tare da daukar hotunansu a duk inda suke rayuwa.