An samu gyara a wutar lantarki

Harkar wutar lantarki ta zama abin da ta zama a baya, yayin da a kwanan nan ake samun ci gaba ta yadda ake mamakin shin wai za mu iya samun wuta kamar haka. Dalilan ba nesa suke ba, an samu sauyin gwamnati, ta hanyar wutar lantarki!Na’uarar tantancewa ta kawo sauyin da aka kasa samu a […]

An samu gyara a wutar lantarki
An samu gyara a wutar lantarki

Harkar wutar lantarki ta zama abin da ta zama a baya, yayin da a kwanan nan ake samun ci gaba ta yadda ake mamakin shin wai za mu iya samun wuta kamar haka. Dalilan ba nesa suke ba, an samu sauyin gwamnati, ta hanyar wutar lantarki!
Na’uarar tantancewa ta kawo sauyin da aka kasa samu a kotu, inda aka gane an ba kamfanoni da dama kwangilolin gyara ga ma’aikatar ta yadda an kashe kudin da ko da babu waya ko daya a Najeriya, sun kai su kawo tsayayyar wuta a kowane gida, duk da yawan jama’ar tarayyar Najeriya.
Wutar lantarki na daya daga cikin abubuwan da talakawa kan mora a kasashe da dama, domin yadda aka kawo da yada ta a birane da kauyuka. Sannan inda muka auna amfanin ta ga rayuwar bil Adama a yau.
Har za a iya cewa wutar lantarki na cikin wajibin rayuwa a yau, ta yadda kusan duk rayuwar bil Adama ta dogara gare ta, ruwan da za mu sha, abincin da za mu ci, nika da sauran hanyoyin sarrafawa, ababen hawa, wayoyi, tufafi mu ma da wutar ake dinka su, da wutar ake sarrafa auduga ta koma yadi, da wutar ake neman ilimi!
Yayin da cin hanci da rashawa suka dabaibayi harkar ta fuskar ba inda ake cin hanci da rashawa kamar a hukumar wutar lantarki gidaje da dama ko ma a ce gidajen da suka fi yawa ba su da bil amma akan kawo masu bil tare da cin su tarar kudin mayar da wuta idan an yanke layin Sannan wasu gidajen akan hada wuta ta karkashin kasa, ta yadda gida daya sai ya ba gidaje goma ko fiye da haka, wannan zai kara wa tiransfoma nauyi, har ta yi bindiga. Kuma wani abin takaicin wasu lokutan da sanin ma’aikatan ake wannan balbalin, ma’aikatan ma’aikatar wuta sun zama kamar wasu ‘yan bala’i. Yayin da suke raba kansu bataliya biyu ko rundunoni don su rikita hankalin mabukata wutar lantarki, inda idan wannan ya zagaya sai dayan ya zagayo duk da nufin karbar abin da za su soke a aljihu. Haka a wasu biranen za ku ga masu kuranga da wayoyi suna yawo a babura, ko su shake kansu akan a kori kura suna bi lunguna. Idan an ci karo da masu jan wuya sai da a yi gaba, yayin da wasu biranen sai sun hada da dan sanda kafin cuwa ta tafi yadda suka so!
Dadin dadawa ma’aikatan kan kafa wa mutane kudin da za su rika biya, wadanda za su rika shiga aljihunsu, ba aljihun gwamnati ko na ma’aikatar. Domin dama su suke yanke wutar, su bar ta wanda yake dadada masu su yanke ta wanda suka ga dama! Ko ba a kawo bil ba, bugu da kari akwai karancin mitoci masu aunawa da kansu, wadanda ake zuba wa kudi, daidai zubin ka, daidai shanka. A wadata wadannan na’urori ga mabukata wutar lantarki a kowane gida, shago da kamfani.
Ya kamata a kawo wata na’ura wadda za ta gane wutar nawa mutum ya sha a wata, ba wai yadda aka saba ba wajen karbar kudin bayin Allah ba tare da wani ma’aunin abin aka yi amfani da ita ba a wani mizani, sai dai karbar kudi kawai! Dole ministan ma’aikatar wuta Fashola ya tsaya tsayin daka don gyara a ma’aiktar wuta ya wuce aikin jiha daya, aikin ne ga tarayyar Najeriya.
Alhamdulillahi wutar lantarki ta fara zama a gidan kowa, mun fara jin dadin na’urorinmu da suka zama abin kallo a wasu lokuta ko talabijin sai dai don ado, ba motsi, a rufe da kura, amma yau sai dai mu yi wa sabuwar Gwamnatin Baba Buhari godiya a bisa gagarumin kokarin kawo karshen duhu, da kawo haske.
Buhari Daure +2347035986444 Muryar Talaka, kofar kaura, Katsina.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno