An samu ingantuwar tsaro kan hanyoyin kasar nan – ’Yan Kasuwar Tumatur
Masu safarar tumatur daga Arewacin kasar nan zuwa Kudanci sun nuna gamsuwar su bisa yadda ake samun ingantaccen tsaro kan hanyoyi, wanda kuma hakan ta sanya ake samun kwanciyar hankali a harkar fataucin tumatur daga Arewacin Najeriya zuwa sauran sassa na kasar nan. Wannan tsokaci ya fito ne daga fataken tumatur da direbobin motocin daukar […]
Masu safarar tumatur daga Arewacin kasar nan zuwa Kudanci sun nuna gamsuwar su bisa yadda ake samun ingantaccen tsaro kan hanyoyi, wanda kuma hakan ta sanya ake samun kwanciyar hankali a harkar fataucin tumatur daga Arewacin Najeriya zuwa sauran sassa na kasar nan.
Wannan tsokaci ya fito ne daga fataken tumatur da direbobin motocin daukar tumatur daga kasuwanni sayar da tumatur na Arewaci zuwa Kudanci dangane da yadda sha’anin tsaro yake inganta a halin yanzu sabanin yadda abin yake a baya.
Sannan sun nunar da cewa yanzu hanyoyin kasarnan sun kasance cikin yanayi na tsaro, kana su kansu masu harkar kai tumatur zuwa wasu sassa suke jin dadin yadda ake gudanar da safararsa daga Arewacin kasar nan zuwa sauran sassa na Najeiya ba tare da gamuwa da matsalolin rashin tsaro kan hanyoyi ba.
Alhaji Abdu Sale,wani mai sana’ar kai tumatur yankin Kudancin kasar nan, ya ce yanzu hanyoyi lafiya lau suke, kuma masu harkar kai tumatur Kudancin kasa suna gudanar da sana’ar su cikin natsuwa da kuma kwanciyar hankali saboda samun tsaro da aka yi a kan hanyoyin.
Haka kuma ya bayyana cewa Gwamnatin Muhammadu Buhari tana kokari kwarai wajen inganta yanayin tsaro a kasar nan, kuma duk wani mai harkar fatauci ko tukin mota daga Arewaci zuwa Kudanci yana ganin wannan ci gaba da aka samu tun zuwan gwamnatin.
Wani direba mai suna Yusuf Lawan, ya shaida wa Amniya cewa direbobi suna aikin su cikin farin ciki, kuma babu wani abu da yake damun su illa rashin kyawun hanyoyi, inda ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta fara aiwatar da gyare-gyare a kan titunan kasar na domin kare rayuka da kuma dukiyoyin al’umma saboda lalacewar da suka yi.
A karshe, Sarkin kasuwar tumatur ta Zaura Malam Rabi’u Abdu Iliyasu ya sanar da cewa yanzu babu wani korafin hanya da direbobi suke kai wa ofishinsa, wanda haka ke nuni da cewa tsaro yana inganta a kowace hanyar mota ta kasar nan, sannan ya ce kasuwanci yana bunkasa, saboda samun tsaro da ake yi a kowane bangare, wanda hakan zai kawo ci gaban tattalin arziki a kasa baki daya.