An samu kan maciji a abincin fasinjojin jirgin sama
Wani bidiyo mai ban tsoro da aka wallafa ya nuna yadda aka samu kan maciji a cikin abincin dare na fasinjoji da ke cikin jirgin sama da ba a san yadda hakan ya faru ba. Fuskar macijin da aka gani a fili tare da idanu, ta kasance a bayyane a cikin tiren abincin da za […]
Wani bidiyo mai ban tsoro da aka wallafa ya nuna yadda aka samu kan maciji a cikin abincin dare na fasinjoji da ke cikin jirgin sama da ba a san yadda hakan ya faru ba.
Fuskar macijin da aka gani a fili tare da idanu, ta kasance a bayyane a cikin tiren abincin da za a bai wa fasinjojin.
- Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram da wasu mayaka 27 a Borno
- Isra’ila ta kashe Falasdinawa 24 a sabbin hare-hare kan Zirin Gaza
Hakan ya faru ne a cikin jirgin saman SunEdpress na ranar Alhamis da ya tashi daga Ankara a kasar Turkiyya zuwa birnin Dusseldorf na Jamus.
Shafin intanet na Kamfanin jirgin sama SunEdpress mai suna Mile One at a Time ya wallafa cewa, “Babban abin fifikonmu ne cewa, mu karrama bakinmu da ma’aikatanmu wajen samar da ingantattun ayyukan da muke yi a cikin jirginmu, ta hanyar nuna inganci da kuma samar da kwanciyar hankali da kwarewa wajen sufuri a jirgi.”
An raba takardar zargezargen da ake tuhumar kamfanin ga manema labarai game da abincin jirgin saman kuma ana yin cikakken bincike game da lamarin.
Har sai an kammala nazari da binciken batun silar ganin kan macijin, tuni an dauki matakan kariya game da al’amarin kuma an samar da abincin jirgin da ya dace.
“Masu yin abincin fasinjoji na jirgin sama na Sancak Inflight Serbices, su ne suka raba abincin jirgin saman amma sun musanta zargin da ake yi, inda suka ce sun tabbatar da cewa an saka kan macijin a cikin abincin ne bayan sun kammala girkin.
“Kamfanin SunEdpress Airlines abokin huldar cinikin fasinjoji ne na cikin kasarmu kuma shahararren kamfanin jirgin sama a Turai, wanda kwanan nan ya yanke shawarar kara fadada harkokin sufurinsa zuwa wasu na’urorin sadarwa.
“Sun sake ba da sanarwar bayar da abinci a cikin jirgi ga fasinjojinsu. Ba mu yi amfani da ko daya daga cikin abubuwan da ake zaton suna cikin abincin ba, lokacin dafa abincin (saboda fasaha da yanayin zafi da ake amfani da su a cikin kayan abincin jirgin).” Kamar yadda jami’an suka sanar.