An samu karanci masu kada kuri’a a zaben Filato

A yau Laraba ne a jihar Filato ake gudanar da zabukan kananan hukumomin jihar, inda rahotanni ke bayyana karancin masu kada kuri’a a mazabun jihar. Zabukan wanda ya gudana a kananan hukumomi 14 cikin 17 na jihar, yayin da aka dakatar da zabukan kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da Riyom da […]

An samu karanci masu kada kuri’a a zaben Filato

A yau Laraba ne a jihar Filato ake gudanar da zabukan kananan hukumomin jihar, inda rahotanni ke bayyana karancin masu kada kuri’a a mazabun jihar.

Zabukan wanda ya gudana a kananan hukumomi 14 cikin 17 na jihar, yayin da aka dakatar da zabukan kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da Riyom da kuma Barikin Ladi.

Gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya yanke shawarar dakatar da zabukan kananan hukumomin ne saboda kalubalen tsaro a yankunan.