An samu kasuwar tallata takaicin soyayya
A wata kasuwar birnin Hanoi da ke kasar bietnam da ake yi wa lakabi da kasuwar ruruwar wutar da masu ciniki na duba wasikun soyayya da turararuka da kyandirori da tsofaffin tufafin da aka aka yi ganiyar soyayya da su, inda ake baje-kolinsu don masoyan da ke fama da kadaici su saya. Mutanen da suka […]
A wata kasuwar birnin Hanoi da ke kasar bietnam da ake yi wa lakabi da kasuwar ruruwar wutar da masu ciniki na duba wasikun soyayya da turararuka da kyandirori da tsofaffin tufafin da aka aka yi ganiyar soyayya da su, inda ake baje-kolinsu don masoyan da ke fama da kadaici su saya.
Mutanen da suka yaukaka soyayya a da kan hadu a kowane wata, don tallata dimbin abin takaicin da ya sosa musu zukata a wata kasuwar kan titi da ke ci a birnin Hanoi, inda suke sayar da kayayyakin da ke tayar musu da hankali saboda alakarsu da soyayyarsu ta da.
Domin a cewar wani mutumin da ya yaukaka soyayya, ta haka ne kawai mutum zai ci gaba da rayuwa. “(bayan rabuwarmu) na dugunzuma cikin bacin rai..amma bayan wani lokaci sai na samu kaina. Abin da ya wuce, ya wuce,” a cewar Phuc Thuy, wanda ya sayar da tufafi da jakunkuna,har ma da mazubin buroshin goge baki da ta samu lokacin da take danyen ganyen soyayya.
Wannan kasuwa naci gaba da bunkasa a duk sa’adda aka budeta a watan Fabrairu, musamman a tsakanin matasan bietnam da ke gudanar da harkokin sshafukan zumunta a intane, wadanda ba sa jin kunya bayyana yadda suke yaukaka dankon soyayya yau da kullum.
“Matasa kan bude cikinsu kan dimbin al’amuran da suka jefa su cikin rudani kan yadda suka shawo kan ciwon lamarin, ba tare da sun sha wahalar soyayayr su kadai,” a cewar wanda ya kafa kasuwar Dinh Thangm, daidai lokacin da masu wakar soyayya ke kada jitar kawata wajen daga gefe.
Ya fara hada-hada a kasuwar ne bayan ya samu wasu mutane kadan da suka yi mummunar rabuwa (a tsakanin masoya) har ta kai ga ba sa sha’awar ganin wani abu da zai tuna musu tsohuwar soyayyar da ta jirga su.
Kuma ya bude kafar sayar da sababbin kaya, sannan yana shiri fgfara irin wannnan jhada-hadar kasuwwanci a babban birnin kasuwanci na kasar bietnam, wato Ho Chi Minh City cikin wannan shekarar.
Yana mai alfaharin baje-kolin wasikun soyayya da katunan murnar zagoyawar ranar haihuwa da tsofaffin guntayen litattafan rubutun sakonnin da tsofaffin masoya suka rika aike wa juna sakonni kafin rabuwarsu.
Dangane da wadanda rabuwarsu ba ta yi munin iriin wadda shiga Thang ya taba dandawa ba, ya baje musu allunan da za su rubuta al’amuran da suka haifar da rabuwatar ta su, don wayar da kai, inda kowane mai tsohuwar soyayya zai fadi abin da ya sa suka rabu.
“Ga daukacin masoyana na da, ina neman afuwa, saboda domin ina jin tamkar ba mu taba sanin juna ba,” kamar yadda aka rubuta a wnai sako da ke nunin da jin kunyar wanda ya rubuta shi.
Wani takaitaccen sakon na kaitsaye cewa ya yi: “Lafiyata kalau!!!”
Thang na fatan ganin maganar rabuwar masoya ta daina zama abin jin kunya, a wannan kasar ’ya kwamunisanci da al’ummarta ke da ra’ayin rikau (rikon al’adu),kuma tsawon zamani an saba da auren hadi.
Yawan al’umar kasar dai ya kai miliyan 93.
Harkokin mu’amalar zamantakewa ta yi matukar samun sauyi saboda kasar ta kulla alaka da duniya t akafar sadarwa, ta yadda dimbin matasa, wadanda suk kwashi kashi 50 cikin 100 na yawan al’umar kkasar da shekarunsu ke kasa da 30 sun rungumi tsarin soyayyyar Yammamcin Turai.
Harkokin sun hada da neman kulla soyayya ta intanet.
“Matasa da dama sukan hadu a shafukan intanet su yi soyayya a intanet, suna kuma iya rabuwa a intanet din,” a cewar Bui Manh Tien, Jami’in shirin tarairayar matasa a karkashin Asusun kula da yawan al’umma na Majalisar dinkin Duniya (UNDP) a kasar bietnam.
A halin yau maza da mata sukan yi matukar jinkirta yin aure, sannan yawan sakin aure na karuwa, kamar yadda alkaluman kididdigar hukuma ya yi nuni.
“Ba ma son sarayar da ’yancinmu, t ahanyar daukar nauyin iyali lokacin da muke amtaswa, muna son jin dadin rayuwarmu kafin aure,” inji Tien matashi dan shekara 25.
A wajen wasu kuwa wannan kasuwa ta masoyan da wutar soyayyarsu tk gushe, wuri ne na kulla sabuwar alaka tasoyayya ko wata harkar ta daban.
“Nakan zo nan don haduwa da mutane, in kuma ga kayayyaki, sannan in yi nazarin abin da ya sanya suke zama abubuwa masu kayatarwa a da,” a cewar Tieu Khuy, kafin ya dauki kwafen makalar Jane Austen, mai taken ‘Alfahari da sukar lamari.’