An samu kifi mai hakoran mutum a gefan teku
Wata mata mai suna Maleah Burrows, mai shekara 31 da danta sun yi gamo da wani kifi mai ban al’ajabi ta yadda kifin ke da hakora irin na mutane a gefan tekun tsibirin St Simon’s Island jihar Georgia da ke Amurka. Matar dai tana tafiya ne da dan nata lokacin da ta hadu da wannan […]
Wata mata mai suna Maleah Burrows, mai shekara 31 da danta sun yi gamo da wani kifi mai ban al’ajabi ta yadda kifin ke da hakora irin na mutane a gefan tekun tsibirin St Simon’s Island jihar Georgia da ke Amurka.
Matar dai tana tafiya ne da dan nata lokacin da ta hadu da wannan kifin bakinsa a bude sai ga hakoran kifin irin na mutane, inda ta ce ba ta tava ganin irin wannan hakoran kifi mai siffar na mutane ba.
Maleah, ta ce ”Sun hadu da kifin ne bayan ruwan tekun ya koro kifin gefan hanya daga cikin ruwa, hakan ya janyo hankalin mu, na tsayawa don ganin yadda kifin ya bude bakinsa“.
Maleah ta kara da cewa, ta dauka kawai wannan kamar irin kifin da ta saba gani ne, amma daga bisani sai na fahimci ba haka ba ne, hakan ya jawo hankali na har na nunawa dan na mai shekaru uku.
A lokacn da nake nunawa da na hakoran kifin, sai da na razana saboda ban tava ganin irin wannan hakoran ba, kifin irin jinsin da aka fi samu a tekunan Amurka an same shi ya mutu kwance bayan ruwan tekun ya koro shi waje, kifin ya kan yi amfani da hakoran wajen datsawa da cin abincin da yake ci.
Wannan kifin da suka gani yana daya daga cikin wanda akasarin masunta ke nema a tekuna.
Maleah `yar asalin garin Charlotte a jihar North Carolina, ta ce wannan kifin yana da nauyi da girman jiki, don haka aka fi neman irinsa.
Bakin kifin duk yana zagaye ne da hakora ba kamar irin na sauran dabbobi ba, a gaban bakin duk ya cika da hakora kamar na mutane.
Da farko na yi mamakin abin da ke bakin, sai ga hakora cike da baki.
Maleah, ta yi tunanin cewa, ”Idan har irin wannan kifin na rayuwa a cikin ruwan da dan’ adam ke shiga, idan ya ciji mutum da wannan hakoran ya zai kasance“.
Duk wanda na nunawa hoton wannan kifin sai ya razana, saboda jama’a da dama ba su tava ganin irin wannan kifin ba.
Irin wannan jinsin kifin yana fara hakora ne lokacin da yake da tsawon mita 4.5mm yana kammala hakoransa lokacin da yake da tsawon mita 15. Kuma kifin zai iya kai girman tsawan santimita 76. An fi samunsa a tekun Gulf da Atlantic na Amurka.