An samu koma-bayan noman alkama a Jihar Katsina
Manoman alkama sun kaurace wa nomanta a bana wanda hakan ya jawo karancin nomanta a bana a wasu yankunan Jihar Katsina. Manoman da suka fito daga shiyyar Funtuwa sun ce noman alkamar a bana ya ja baya sosai ba kamar shekarun baya ba, hakan ya faru ne saboda ba ta bayar da yabanya mai kyau […]
Manoman alkama sun kaurace wa nomanta a bana wanda hakan ya jawo karancin nomanta a bana a wasu yankunan Jihar Katsina. Manoman da suka fito daga shiyyar Funtuwa sun ce noman alkamar a bana ya ja baya sosai ba kamar shekarun baya ba, hakan ya faru ne saboda ba ta bayar da yabanya mai kyau sannan ga karancin farashi a kasuwa idan aka kwatanta da tumatir.
Shekara uku da suka wuce an samu karin noman alkamar a yankin domin farfado da martabar kayan amfanin gonarmu na gida.
Kamar yadda manoman suke cewa, noman alkamar bai kai karfi da karbuwar noman shinkafa ba; hakan ya sa mafi yawan manoman suka kaurace mata.
Malam Aminu Maikudi na daya daga cikin manoman alkama daga shiyyar Funtuwa ya ce, “yanzu noman shinkafa ya fi zama tabbas, wanda kuma shi ne gwamnati ta fi mayar da hankalinta a kai fiye da na alkama, hakan ya haifar da rage tagomashinta. Shekara biyu da suka wuce, an rika barinmu da ita, sai abin da kasuwa ta nuna, amma Allah cikin rahamarSa bai sa mun fadi ba, domin mun karu ta bangaren noman tumatir.
“Idan ana so manoma su rungumi noman alkama, to gwamnati ta bullo da wani shiri da zai shafi batun farashi tare da tallafa wa manoman,” inji shi.
Shi kuwa Malam Musa Auwal, daga yankin Dandume ya ce, bai ga abin da zai ja hankalinsa ba da zai sa ya noma alkama. “Muddin kana noma tumatir da albasa da kabeji da sauransu babu abin da zai sa in koma ga noman alkama in aka kwatanta farashinsu a kasuwa. Hekta daya in ka noma ta alkama, mafi yawan abin da zai ba ka shi ne buhu 12, in kuwa dankalin Turawa ne za ka samu buhu 30. Sannan manoman tumatir gaskiya za su yi dariya domin tun yanzu an fara ganin alamu fiye da shekarun baya. A cikin wannan mako kawai an sayar da babban kwandon tumatir Naira 2,700 a farashin cikin gona ba na kasuwa ba. Yawan ruwan saman da aka samu da kuma batun rufe kan iyakoki da ake ciki, ya nuna cewa manoman tumatir za su kara samun kudin shiga,” inji shi.
Bincike ya nuna, ana sayar da buhun alkama a kan Naira dubu 23, amma akwai yiwuwar farashin ya karu nan gaba saboda karancinta da ake samu a yanzu.