An samu kwantacce dan shekara 44 a cikin wata mata a kasar Brazil

Wata mata ’yar asalin kasar Brazil da ta dauki ciki shekara 44 da suka gabata, likitoci sun tabbatar mata da cewa akwai kwantaccen jariri a cikinta, daidai lokacin da ta cika shekara 84. Matar ta fara jin zafin ci  mararta ne, don haka ta nufi asibiti, inda likitoci suka bayyana mata akwai daskararren jariri a […]

An samu kwantacce dan shekara 44 a cikin wata mata a kasar Brazil

Wata mata ’yar asalin kasar Brazil da ta dauki ciki shekara 44 da suka gabata, likitoci sun tabbatar mata da cewa akwai kwantaccen jariri a cikinta, daidai lokacin da ta cika shekara 84. Matar ta fara jin zafin ci  mararta ne, don haka ta nufi asibiti, inda likitoci suka bayyana mata akwai daskararren jariri a cikinta, don haka ta cije hakora hart a kusa faduwa a kasa
Hakuikanin abin da hoton cikin matar ya nuna, shi ne daskararren jariri kamar dutse. Irin wannan cutar ba a saba ganinta ba, inda dan tayi zai bunkasa a cikin, sabanin mahaifa. dan tayin jariri ya mutu ne a sanadiyyar rashin gudanar jini,  a tsakaninsa da mahaifiyarsa. A irin wannan yanayi aikin fida aka yi wa uwa a cire mata jariri, idan har ba a cire ba shi ne yake daskarewa ya zama dutse a cikin uwa.
A cewar Dokta Kim Garci, wani likita a ke asibiti Jami’ar Clebeland, “irin wannan yanayi sau 300 aka taba samun a tarihin ayyukan likitanci.” Sau daya ake samun haihuwar jaririn da ya rayu a cikin uwa cikin mutum dubu 10. A zamanin da, masu kula da lafiya kan yi tunanin cikin ya zube ne, tunda cikin uwar ya daina girma. Sun yi kuskure, domin jariribn katsaya ne a tsakanin cinyoyinta, har ya daskare ya zama dutse.
A Turancin likitanci, ana amfani a Kalmar Girikanci don kwatanta irin wannan jariri, wanda ake yi wa lakabi da ‘lithopedion.’  Bayan da jaririn ya mutu, garkuwar jikin uwa za ta yi ta aiki wajen ba ta kariya daga mataccen jaririn. Don haka wannamn uwar take dauke da wannan jariri a cikinta har tsawon shekara 40!
Hoton sassan jikin mutum na d-ray, ya yi nuni da kafadu da kafafuwa da kasusuwan jikin daskararren jariri na tsawon shekara 44, har ma da kasusuwan uska da na hakarkari. Likitoci na ganuin jaririn ya mutu ne a tsakanin makonni 20 zuwa 28. Sai dai wannan uwa ’yar Brazil ta zabi ta ci gaba da zama daskakararen jaririn tsawon rayuwarta.
Watanni biyu da suka gabata, an taba smaun irin wannan matsalar daskakararen jariri a kasar Kwalombiya, amma wannan uwar ’uyar shkara 82, ta bukaci a yi mata aiki, a cire shi daga cikinta, kamar yadda shafin sadarwa na naturalnews.com ya ruwaito.