An samu mabaraci da Naira dubu 250 a Saudiyya
Hukumar yaki da bara ta kasar Saudiyya, ta kama wani mabaraci, dan kasar Yemen da Riyal dubu 50 a aljihunsa. Mutumin dan shekara 45, an same shi yana rokon wata mata ta ba shi sadakar kudi. Jami’an hukumar sun ce mutumin, wanda ba shi da takardun zaman kasa, yana sanye da tsumman tufafi, don mutane […]
Hukumar yaki da bara ta kasar Saudiyya, ta kama wani mabaraci, dan kasar Yemen da Riyal dubu 50 a aljihunsa. Mutumin dan shekara 45, an same shi yana rokon wata mata ta ba shi sadakar kudi. Jami’an hukumar sun ce mutumin, wanda ba shi da takardun zaman kasa, yana sanye da tsumman tufafi, don mutane su ji tausayinsa.
Ma’aikatar kula da jin dadi da walwalar al’umma, mna ta fadakar da mutane kan su daina bai wa irin wadannan mutane kudi.