‘An samu mace-macen mata msu juna-biyu sau 872 cikin wata 6 a Bauchi’

An sami adadin ne a asibitoci 123 a cikin wata 6

‘An samu mace-macen mata msu juna-biyu sau 872 cikin wata 6 a Bauchi’

Wata mace mai juna biyu (Tsohuwar ajiya)

Hukumar Kula da Asibitocin Sha-ka-tafi ta Jihar Bauchi ta ce an samu mace-macen mata masu juna-biyu da barin ciki har sau 872 cikin watanni shida a jihar.

Hajiya Jummai Inuwa, ta sashin lura da bincike da habaka lafiyar mata masu juna biyu ta jihar Bauchi (MPDSR) ce ta bayyana hakan yayin taron bita na kwanaki biyu da hukumar ta shirya a jihar.

Ta ce an sami adadin ne a asibitoci 123 da ke fadin Jihar.

A cewarta, “MPDSR ta jihar Bauchi ta samu rahoton mutuwar mata 56 da bari 816 daga watan Yuli zuwa Disamba 2022.

“Mun tattaro wadannan alkaluman ne daga asibitocin sha-ka-tafi 123, da manyan asibitoci 20.

“Manyan asibitoci na Toro, da Ningi, da Azare ne suka fi samun mace-macen da jimillar mutane 31″, in ji ta.

A nasa bangaren, Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Bauchi, Ali Babayo, ya bukaci hukumomin kiwon lafiya da su himmatu wajen ganin an samu ci gaba a fannin, da inagnata banagaren da ke bukatar hakan.