An samu macen farko da ta zama babbar Editar jarida a Saudiyya

Wata mace mai suna Somayya Jabarti ta zama babbar Editar jarida ta farko a kasar Saudiyya. Sumayya dai ta taba zama mukaddashin Editar Jaridar turanci ta Saudi Gazette. Kuma tana rike da tsohon mukaminta  a daidai lokacin da Baban Editan jaridar mai barin gado ya bayyana nadata kan wannan mukami.“An samu tsaga a saman rufin […]

An samu macen farko da ta zama babbar Editar jarida a Saudiyya

Wata mace mai suna Somayya Jabarti ta zama babbar Editar jarida ta farko a kasar Saudiyya. Sumayya dai ta taba zama mukaddashin Editar Jaridar turanci ta Saudi Gazette. Kuma tana rike da tsohon mukaminta  a daidai lokacin da Baban Editan jaridar mai barin gado ya bayyana nadata kan wannan mukami.
“An samu tsaga a saman rufin gilashi, wanda nike fatan ya zama kofa,” a cewar Somayya Jabarti a lokacin da ta kama ragamar aiki, kamar yadda kafar labarai ta Arabiya News ta ruwaito.
Ta ce: “Kasancewata macen farko da ta zama Babbar Editar jarida, nauyin da ya rataya a kaina ribi biyu ne. Domin duk abin da na aikata zai zama ma’aunin dabi’ar matan Saudiyya.
Jabarti ta ce daukacin wakilan jaridar Saudi Gazette 20, m,utum uku ne kawai maza, amma manyan mukamai duk maza ke rike da su.
“Mafi yawan wakilanmu mata ne, wannan ba yana nufin mun fifita mata ba ne a kan maza, a’a. Sai dai akwai dimbin mata da ke sha’awar zama ’yan jarida,” injita.
Ta ce: “Ba a kai ga makurar cimma nasara ba, har sai nag a tsararraki na, wadanda su ma mata ne a Saudiyya sun rike mukaman da za su damar fada a ji.”
Babban Editan Jaridar Saudi Gazette mai baring ado, Khaled Almaeena, ya baza wa duniya labarin maye gurbinsa da Sumayya Jabarti, kamar yadda jaridar The Guardian ta Landan ta ruwaito.