An samu mai cutar coronavirus na farko a jihar Sokoto

An samu mutum na farko da aka tabbatar ya kamu da cutar coronavirus a jihar Sakkwato. Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a birnin Sakkwato. “Ina bakin cikin sanar da al’ummar jihar Sakkwato cewa an samu bullar cutar coronavirus a jihar Sakkwato. “Mutumin da […]

An samu mai cutar coronavirus na farko a jihar Sokoto

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato

An samu mutum na farko da aka tabbatar ya kamu da cutar coronavirus a jihar Sakkwato.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a birnin Sakkwato.

“Ina bakin cikin sanar da al’ummar jihar Sakkwato cewa an samu bullar cutar coronavirus a jihar Sakkwato.

“Mutumin da ya kamu da cutar ya fara  karbar magani  a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo, kuma bayan an tabbatar da ya kamu an kai shi wurin killace masu dauke da cutar a cibiyar bayar da magani dake Amanawa”, inji Gwamna Tambuwal.

Gwamnan ya yi kira ga mutanen jihar Sakkwato su zama masu biyayya ga duk wani umarni da jami’an lafiya za su bayar don ganin cutar ba ta yadu ba.

Tambuwal ya ce “abin da muke ji ne yanzu kuma ya zo mana – akwai bukatar mu tashi tsaye a matsayinmu na gwamnati da ’yan kasa mu ga wannan cutar ba ta watsu ba. Ina kira ga jama’a su girmama duk matakin da za mu dauka idan lokacin yin hakan ya taso domin kubutar al’umma gaba daya a jiha.

“Akwai yiwuwar daukar matakai nan gaba”, inji shi.

Tambuwal ya ce akwai bukatar goyon baya da hadin kai domin a gudu tare a tsira tare, sannan ya roki Allah ya taimake su wajen shawo kan cutar ba tare da ta yadu ba.

Sakkwato ta zama jiha ta baya-bayan nan da aka bayar da sanarwar bullar cutar a Najeriay.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno