An samu masu bautar marakin da aka haifa da kai biyu
Bayan haihuwar wani dan maraki da kai biyu a Lardin Buriram da ke kasar Thailand, mamallakin saniyar mai suna Somorn Krasaesom ya yi ikirarin cewa, ya lashe kudin da ya kai Fam 500 (kimanin Naira dubu 264) na kudin caca. Jama’ar kauyen sun yi ta tururuwa zuwa ganin dan marakin mai kai biyu, wanda hakan […]
Bayan haihuwar wani dan maraki da kai biyu a Lardin Buriram da ke kasar Thailand, mamallakin saniyar mai suna Somorn Krasaesom ya yi ikirarin cewa, ya lashe kudin da ya kai Fam 500 (kimanin Naira dubu 264) na kudin caca.
Jama’ar kauyen sun yi ta tururuwa zuwa ganin dan marakin mai kai biyu, wanda hakan ya sa mamallakin marakin ya gina wajen bauta a gidansa don jama’a su bauta wa dan marakin.
- Daga Jangebe ba za a sake sace dalibai a Najeriya ba – Buhari
- Mukabala: Sheik Abduljabbar ya amsa gayyata, ya gindaya sharudda
Wannan dan maraki da aka haifa da kai biyu da wadansu mazauna kauyen suka yanke shawarar bauta masa, sun amince cewa bautar irin wannan dan maraki mai kai biyu alama ce ta samun nasara da fatar samun abu mai kyau a gaba.
A cikin rahoton an bayyana yadda masu bautar suke kunna wuta a gaban dan marakin kafin su roki abin da suke bukata.
An haifi dan marakin ne a ranar 14 ga Fabrairun bana wanda ya zo duniya da kai biyu da karin kunne daya da ke tsakiyar kawunan biyu.
Dan marakin yana da wata nakasa a jikinsa, inda yake samun matsalar numfashi sannan yana jin kasala yayin cin abinci.
Mamallakin saniyar mai suna Somorn Krasaesom wanda manomi ne mai shekara 66, ya dauki dan marakin zuwa asibiti, bayan kai shi asibiti, da likitoci suka duba shi cikin rabin awa sai ya mutu.
Somorn ya ce, mutuwar dan marakin ta sa rayuwarsa ta lalace “Amma samun dan marakin da aka haifa da kai biyu wata kyauta ce daga sama.
“Ban taba mafarkin samun irin wannan dan maraki ba.”
“Na kasance ina kula da dan marakin kamar jikana. Wannan dan maraki na sa ran zai kawo min wadata a rayuwata.”
A cewar Somorn yayin bayyana mafarkin da ya yi, “Haihuwar dan marakin ta zama gaskiya don tunda saniyar take haihuwa ban taba samun sa’ar irin wannan halitta ba, na yi sa’a,” inji Somorn.
A yanzu haka dai Somorn yana shirin adana gawar dan marakin tare da gina masa wajen bauta a kusa da gidansa.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake samun wata dabba na haihuwar mai kai biyu ba, inda aka rika wallafa rahotannin a shafukan Intanet.
A kwanakin baya wani mai kare ya sanar da cewa karensa ya haifi dan kwuikuyo mai ido daya. Kuma an rada wa karen suna da Cyclops saboda bai da hanci, a haka yake kokarin ya sha nono daga wajen uwarsa.
A maimakon binne karen sai mai karen ya adana gawar karen a lambu, daga nan ya sanya gawar a cikin akwatin gilashi don tunawa da shi.