An samu mata masu juna biyu 2,239 dauke da kanjamau a Jihar Kaduna

Kimanin mata masu juna biyu 2,239 ne aka tabbatar sun kamu da cutar kanjamau bayan yi musu gwaji a bara a Jihar Kaduna. Wani rahoto da aka fitar kan halin da ake ciki game da dakile yaduwar cutar kanjamau daga uwa zuwa ga jaririnta (PMTCT) dauke da sanya hannun Sakataren Shirin PMTCT, Malam Lawal Abubakar […]

An samu mata masu juna biyu 2,239 dauke da kanjamau a Jihar Kaduna
An samu mata masu juna biyu 2,239 dauke da kanjamau a Jihar Kaduna

Kimanin mata masu juna biyu 2,239 ne aka tabbatar sun kamu da cutar kanjamau bayan yi musu gwaji a bara a Jihar Kaduna.

Wani rahoto da aka fitar kan halin da ake ciki game da dakile yaduwar cutar kanjamau daga uwa zuwa ga jaririnta (PMTCT) dauke da sanya hannun Sakataren Shirin PMTCT, Malam Lawal Abubakar ne ta bayyana haka.
Malam Lawal ya ce mata 377 daga cikinsu sun fito ne daga karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, sai 262 daga Chikun, 237 daga Kachia da 213 daga Zariya, yayin da Kudan take da mafi karanci da mutum takwas. Sauran su ne karamar Hukumar Kauru 11 sai kaura16 na mata masu juna biyu da aka yi wa gwajin kanjamau a bara.
Bayanai sun nuna cewa mata masu juna biyu 764 daga cikin 2, 239 suka koma asibitocin da suke gudanar da shirin PMTCT a jihar don kula da su. Kuma sanarwar ta ce wadanda suka ki komawa sun yi haka ne saboda tsoron kada a rika nuna musu kyama, yayin da sauran suka ki shaida wa mazajensu saboda tsoron kada su sake su.
Ya ce an yi shirya za a cimma kashi 70 cikin 100 na gwajin kanjamau ga mata masu juna biyu amma abin takaici kananan hukumomi bakwai kacal ne daga cikin 23 suka cimma wannan adadi.
Ya ce an kara cibiyoyin yaki da yada cutar kanjamau daga uwa zuwa jariri a jihar daga 37 a shekarar 2007 zuwa 475 a shekarar 2014, amma duk da haka ana samun karancin amfani da su wajen neman shawara da yin gwajin cutar a jihar.
Rahoton ya ce shiyyar Sanata ta Tsakiya ne ta fi karancin mata masu zuwa gwajin kanjamau da neman shawara da kimanin kashi 48 cikin 100, sai shiyyar Kudu mai kashi 54, yayin da shiyyar Arewa ke da kashi 61 a shekarar 2014, inda ya kara da cewa, duk da haka an samu karin ci gaba da kashi 40 cikin 100 zuwa kashi 54 a shekarar 2014.