An samu mutane cikin mawuyacin hali a wani gida a Ibadan

A karshen makon jiya ne rundunar ‘yan sandan Jihar Oyo ta gano wani gida a  kusa da birnin Ibadan da aka daure wadansu mutane maza da mata su 15 da sarka a kafafuwansu, wadanda suka kanjame da  kuma rubabbun gawarwaki a yashe da kasusuwan kwarangwal na mutane da aka cunkusa a cikin wata rijiya da […]

An samu mutane cikin mawuyacin hali a wani gida a Ibadan

A karshen makon jiya ne rundunar ‘yan sandan Jihar Oyo ta gano wani gida a  kusa da birnin Ibadan da aka daure wadansu mutane maza da mata su 15 da sarka a kafafuwansu, wadanda suka kanjame da  kuma rubabbun gawarwaki a yashe da kasusuwan kwarangwal na mutane da aka cunkusa a cikin wata rijiya da suturu da takalma da jikkuna da lambobin wayar hannu da katunan shaidan mutane da aka tara su a cikin wani kontina dake girke a cikin wannan gida da ba a kammala ginawa ba a unguwar Soka da ke Idi Mangoro.
A ranar Litinin  Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo ya gayyaci Kwamishinan ‘yan sanda Muhammad Abdulkadir Indabawa da kwamandan jami’an tsaro na SSS, Mista Chals Ugwu, suka rufa masa baya zuwa wannan gida domin gane wa idanunsu komai.
 Kafin tawagar Gwamnan ta isa wannan wuri sai da wadansu mutane suka yi zanga-zangar lumana, har wadansu suka yi yunkurin shiga cikin gidan amma ‘yan sandan da aka girke a wajen suka hana su, wanda hakan ya haifar da tayar da jijiyar wuya da tayi sanadin harbin bindiga da ya kai ga mutuwar wata mata wadansu kuma suka samu raunuka.  Masu zanga-zangar sun lalata motoci masu yawa da ke wucewa a kan hanyar Edpress ta Ibadan zuwa Legas. Amma isowar Gwamnan ke da wuya sai ya fara neman tawagar tashi su yi tsayuwar minti 1 domin nuna alhini da tausayin irin barnar da aka tafka a cikin wannan gida da mutuwar wannan mata.
Da yake lallashi da ba su hakuri, Gwamnan ya yi wa mazauna wannan unguwa ta Soka, Idi Mangoro, alkawarin daukar mutanensu kai tsaye. Kuma a fusace, a nan take ya bayar da umarnin soke takardar mallakar gida  (C of O) na wannan gida da ake boye mutanen da aka sato, kuma ya ce a hanzarta rushe ginin gidan.
 A zantawar da ya yi da wakilinmu, Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Oyo, Muhammad Abdulkadir Indabawa ya ce, “akwai mutanen da muka samu a daure a cikin gidan da ake zargin cewa ana yi musu maganin ciwon tabin hankali ne, amma yanzu haka muna ci gaba da bincike domin gano gaskiya.” Ya ce binciken ne zai nuna musu gaskiya, shin maganin ciwon hauka ake yi wa daurarrun mutanen ko kuwa sato su aka yi? ‘’Mun kama mutum daya da yake gadin gidan tare da wadansu mutane da ke zaune a kusa da gidan, wadanda muke yi musu tambayoyi dangane da wannan al’amari.”
 A binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa akwai da yawa daga cikin mazauna unguwar Soka, Idi Mangoro da ke kusa da Ibadan sun dade da samun labarin irin barnar da ake yi a cikin wannan gida da ba a kammala ginawa ba, amma suna jin tsoron sanar da mahukunta. An bankado asirin gidan ne a karshen makon jiya a lokacin da wadansu mutane suke cigiyar dan uwansu mai sana’ar Okada, da suka kusanci wannan wuri sai suka rika jin hayaniya a cikin gidan, da suka shiga sai suka tarar da mutane maza da mata a daure da sarka a kafafunsu. A nan take suka sanar da jami’an tsaro, wadanda suka kai dauki tare da gano sauran abubuwa na ban tausayi, kamar wani mutumi kwance a kasa kudaje na yawo a cikin bakinsa da wata mata da ta ce daga jihar Edo ta fito kuma ta yi shekaru 10 ke nan a cikin gidan.
 daya daga cikin mutanen da aka daure a kafa da aka kwance shi sai ya garzaya a guje ya fice daga cikin gidan yana kururuwa yana cewa shi bai taba samun ciwon hauka ba. Ya ce kama shi aka yi lokacin da yake bara aka kawo shi cikin wannan gida.