An samu nasara a yaki da cutar Sankarau a Afirka

Hukumar lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa an kusa kawar da cutar Sankarau a kasashen Afirka amma ta gargadi cewa cutar na iya dawo wa muddin kasashen suka kauce wa ci gaba da karbar sabon allurar riga-kafin cutar akai-akai, kamar yadda gidan rediyon RFI ya bayyana.Kimanin shekaru biyar ke nan da aka fara wayar […]

An samu nasara a yaki da cutar Sankarau a Afirka
An samu nasara a yaki da cutar Sankarau a Afirka

Hukumar lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa an kusa kawar da cutar Sankarau a kasashen Afirka amma ta gargadi cewa cutar na iya dawo wa muddin kasashen suka kauce wa ci gaba da karbar sabon allurar riga-kafin cutar akai-akai, kamar yadda gidan rediyon RFI ya bayyana.
Kimanin shekaru biyar ke nan da aka fara wayar da kan jama’a dangane da karbar allurar rigakafin cutar a kasashen Afirka da suka fi fama da cutar wadda ta yadu daga Senegal da Habasha zuwa sauran kasashen nahiyar.
Hukumar WHO ta ce an samu gagarumar nasara wajan yaki da cutar, amma da yiwuwar cutar ta kara tsananta nan da shekarar 2030 matukar an dakatar da karbar allurar rigakafin.
An samar da samfurin sabuwar allurar rigakafin ta ne bayan ministocin lafiya na kasashen nahiyar sun bukaci hakan a lokacin da cutar ta barke a shekarar 1996, inda ta kama fiye da mutane dubu 250 baya ga hallaka mutane fiye da dubu 25 a cikin watanni.
Tun daga shekarar 2010, an yi nasarar yi wa mutane fiye da miliyan 237 allurar a kasashe 16 cikin 26 da ke fama da cutar.
A shekarar 2013 an samu mutane hudu kacal dauke da cutar a daukacin kasashe 26 da ke fama da ita.