An samu nasarar gwajin na’urar tantance katin zabe
Kwamishinan Hukumar Zabe na kasa (INEC) Injiniya Nura Yakubu ya ce amfanin da na’urar tantance masu kada kuri’a a lokacin zabe ita ce hanyar da za ta magance aringizon kuri’a a lokacin zabe. Injiniya Nura Yakubu ya bayyana haka ne bayan kammala zaben gwaji da hukumar ta kasa ta gudanar a wasu mazabu a garin […]
Kwamishinan Hukumar Zabe na kasa (INEC) Injiniya Nura Yakubu ya ce amfanin da na’urar tantance masu kada kuri’a a lokacin zabe ita ce hanyar da za ta magance aringizon kuri’a a lokacin zabe.
Injiniya Nura Yakubu ya bayyana haka ne bayan kammala zaben gwaji da hukumar ta kasa ta gudanar a wasu mazabu a garin Mutum Biyu da ke karamar Hukumar Gassol a Jihar Taraba a karshen mako.
Ya ce kowa ya gamsu da yadda na’urar tantance masu kada kuri’a suke aiki kuma ba a samu wani bata lokaci wajen tantance masu jefa kuri’a da suka fito ba.
Kwamishinan ya ce yadda jama’a suka fito waje gudanar da zaben gwajin ya nuna cewa za a samu fitowar jama’a a lokacin babban zabe kamar yadda ya kamata.
Ya ce ’yan kura-kuran da aka samu a zaben gwajin inda na’urar ta kasa gane zanen hannun wasu masu katin zabe ya auku ne saboda hannun masu katin ya yi kaushi ko an sun yi lalle.
Ya ce akwai bukatar mata su guji yin lallae ko kunshi akalla mako daya kafin ranar zabe su kuma masu kaushin hannu su goge hannunsu yadda kaushin zai ragu ta yadda na’urar za ta gane layin yatsunsu.
Wasu daga cikin wadanda suka yi gwajin zabe sun nuna gamsuwa da yadda na’urar tantance katin zaben take yin aiki a cikin karamin lokaci.
daya daga cikinsu Alhaji Jidda Yusuf ya bayyana wa wakilinmu cewa a cikin karamin lokaci na’urar ta tantance katin zabensa da ta maidakinsa wadda ke bayansa.
Alhaji Jidda ya ce in haka na’urar za ta yi aiki a lokacin babban zabe, to, lallai ba za a samu wani bata lokaci ba wajen gudanar da zaben.
A Jihar Nasarawa kuwa hukumar ta gudanar da zaben gwajin ne a Garaku hedikwatar karamar Hukumar Kokona inda aka samu gagarumar nasara.