An samu raguwar Ebola a Liberiya – Hukumar Lafiya

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce an samu raguwar wadanda suka kamu da cutar Ebola a kasar Liberiya a makon jiya. Sai dai an samu karuwar mutanen da suka kamu da cutar da zuwa 132 a kasashen Guinea da kuma Saliyo, adadin da ya rubanya wanda ake da shi sau hudu a makonnin da […]

An samu raguwar Ebola a Liberiya – Hukumar Lafiya
An samu raguwar Ebola a Liberiya – Hukumar Lafiya

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce an samu raguwar wadanda suka kamu da cutar Ebola a kasar Liberiya a makon jiya.

Sai dai an samu karuwar mutanen da suka kamu da cutar da zuwa 132 a kasashen Guinea da kuma Saliyo, adadin da ya rubanya wanda ake da shi sau hudu a makonnin da suka wuce.
A rahoton baya-bayan nan da hukumar WHO ta fitar kan barkewar cutar Ebola a yammacin Afirka, ta ce an samu karuwa a adadin wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar kamuwa da cutar a kasashen Guinea da Saliyo. Ta ce a wadannan kasashe ba a kebe wadanda suka kamu da cutar da gaggawa, haka kuma ba a fahimci yadda za a yi wa masu dauke da cutar magani ba.
Ya yin da hukumar ba da agaji ta Majalisar dinkin Duniya ta ce har yanzu ana ci gaba da binne gawawwakin wadanda suka mutu ba bisa ka’aida ba.
Cutar Ebola dai ta hallaka mutane fiye da 10,000 a yammacin Afirka, inda cutar ta fi kamari tare da yin mummunar barna a kasashen Liberiya, da Guinea da kuma Saliyo. Ya yin da kasashen Senegal da Nageriya da kuma Mali suka shawo kan cutar baki daya.